logo

HAUSA

Tafiya Sannu-Sannu Kwana Nesa

2021-09-29 19:55:50 CRI

Tafiya Sannu-Sannu Kwana Nesa_fororder_微信图片_20210929194339

BY CRI HAUSA

Yanzu kasar Sin ta tashi daga matsayin kasa mai fama da yanayi na talauci zuwa kasar da al’ummarta ke rayuwa cikin matsakaiciyar wadata. Gwagwarmayar da JKS ta jagoranta bisa hadin kan al’ummar Sinawa ita ce ta kai kasar ga hawa tudu mun tsira. Mai hakuri aka ce ya kan dafa dutse har ma ya sha romonsa.

A kan auna matsayin al’umma mai matsakaicin wadata ta fannonin da suka shafi ilimi, da tattalin arziki da ababan more rayuwa, da tsaro da sauran muhimman fannonin rayuwa na yau da kullum. Baya ga nasarar da kasar ta cimma a fannonin inganta rayuwar jama’a, haka kuma Sin ta yi fice a fannonin kimiya da fasaha da kirkire-kirkire da binciken sararin samaniya, baya ga irin gagarumar gudummawar da har yanzu take baiwa duniya a fannin yaki da annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya.

Bayan da duniya ta shaida nasarar da kasar Sin ta cimma wajen samar da al’umma mai matsakaiciyar wadata a dukkan fannoni, ya sa ranar Talata 28 ga watan nan na Satumba, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani, don yin bayani kan yadda kasar ta kai ga cimma wannan gagarumar nasara ta gina al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowane fanni, ko Xiaokang da Sinanci

Ita dai wannan takardar mai taken "Fadi tashin kasar Sin daga talauci zuwa wadata," ta yi bayani dalla-dalla cewa, tabbatar da wadataccen wadata ta kowane fanni, kamar yadda aka ayyana a watan Yuli, alama ce mai matukar muhimmanci dake nuna farfadowar kasar. Matakin dake kara tabbatar da matsayin kasar na zama ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, bayan kasar Amurka.

Takardar ta kuma yaba da aiki tukuru da JKS da jama'ar Sinawa suka yi, sannan ta kalli nasarar da kasar Sin ta cimma wajen tabbatar da wadata ta hanyar samar da ci gaba ga kowa da kowa a fadin kasar.

Dangane da tabbatar da wadatacciyar wadata ta kowane fanni a matsayin babbar gudummawar da Sin ta ba duniya, takardar ta kuma yi bayanin yadda duniya za ta ci gajiyar ci gaban kasar Sin, kamar yadda kullum mahukuntan kasar Sin ke jaddada cewa, burinta shi ne samar da gudummawa don raya kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.

A matsayinta na kasa mafi yawan jama'a, kana babbar kasa mai tasowa a duniya, kasar Sin ta ba da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya ta hanyar samun matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni.

Nasarar da kasar Sin ta cimma ta kafa al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni, ta taimaka matuka wajen rage yawan mutanen da ke fama da talauci a duniya tare da samun sabbin dabaru na gogewa a fannin zamanantar da bil Adam, a hannu guda kuma shirinta na bude kofa ga ketare ya inganta hadin gwiwar samun nasarar moriyar juna. (Ibrahim Yaya)