logo

HAUSA

Me ya sa kasar Sin ke samun karbuwa tsakanin kasashen Afirka?

2021-09-29 18:55:16 CMG

A ranar Juma’a mai zuwa za a yi bikin murnar cika shekaru 72 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. Cikin wadannan shekaru 72 da suka gabata, kasashen Afirka da kasar Sin na kokarin raya hadin gwiwa da juna, a fannonin neman ‘yancin kai da raya tattalin arziki. Sai dai tambayar ita ce: Me ya sa kasar Sin ke kara samun karbuwa tsakanin kasashen Afirka? Zan iya amsa wannan tambaya da wasu labaru guda 2 da na karanta a kwanan nan.

Me ya sa kasar Sin ke samun karbuwa tsakanin kasashen Afirka?_fororder_1

Wani labari ya shafi kasar Najeriya. Kamfanin Star Times na kasar Sin ya fara gabatar da wasu jerin wasannin kwaikwayo na telabajin mai taken “Okirika”, wanda ya shafi zaman rayuwar mutane marasa karfi miliyan 87 na kasar Najeriya, inda ya nuna yadda suke fara’a, da kokarin kyautata rayuwarsu. Wasan kwaikwayon da ya samu yabo sosai daga kafofin yada labarai na kasar, ganin yadda aka mai da hankali kan zaman rayuwar jama’ar Najeriya, da kokarin ba su kwarin gwiwa. Ban da samar da wadannan wasannin kwaikwayo, kamfanin Star Times ya ce zai taimakawa dimbin matasan Najeriya da suka kware samun damammakin raya harkokinsu a Nollywood.

Me ya sa kasar Sin ke samun karbuwa tsakanin kasashen Afirka?_fororder_2

Sai kuma wani labari da ya faru a kasar Sin. Kwanan nan aka gudanar da wani biki na tallata kayayyakin kasashen Afirka ta hanyar hotunan bidiyo kai tsaye ta kafar Internet a birnin Chang’sha dake kudancin kasar Sin, inda a cikin dakunan watsa bidiyo fiye da 10, akwai wasu samari da ‘yan matan kasar Sin da suka yi kokarin sayar da gahawar kasar Habasha, da ridi na kasar Tanzania, da farin garin yaji na kasar Kamaru, da dai sauransu. Hakika wadannan samari da ‘yan mata suna aiki ne a wata cibiyar raya harkar kasuwanci ta shafukan Internet, wadda bayan kafuwarta ta gabatar da bukukuwan tallata kayayyakin kasashen Afirka 4200, inda aka yi nasarar sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai fiye da dalar Amurka miliyan 85.

Wadannan labarai 2 sun nuna wani yanayi na musamman da kasar Sin take ciki, yayin da take hulda da kasashen Afirka, wato kasar ta lura da bukatu na jama’ar kasashen Afirka, da kokarin samar musu da alfanu. Wannan sahihanci ya sa kasar Sin ke samun karbuwa tsakanin kasashen Afirka, da taimakawa wajen yaukaka huldar dake tsakaninsu a kai a kai.

Hakika wannan sahihancin da kasar Sin ta nuna ma kasashen Afirka, yana da nasaba da tunanin Sinawa na darajanta dan-Adam. A kasar Sin, jam’iyya mai mulki, wato jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatin kasar, suna dora cikakken muhimmanci kan samar wa jama’a da moriya, da kokarin inganta zaman rayuwarsu. A nasu bangare, jama’ar kasar suna goyon bayan jam’iyyar mai mulki da gwamnati, da son taimaka musu gudanar da mulki da kyau. Wannan tunani na hadin kai, ya  taimaka wajen kara hada kan mutanen kasar Sin fiye da biliyan 1.4 waje guda, ta yadda suka zama wata hadaddiyar al’umma, tare da tabbatar da moriyarsu baki daya. Wannan tunani ne na neman hadin kai da tabbatar da moriyar juna ya sa kasar Sin ke iya nuna sahihanci ga kasashen Afirka, da samar musu da ainihin alfanu, da damar samun ci gaba. Hakan shi ne ainihin dalilin da ya sa kasar Sin ta samu cikakkiyar karbuwa tsakanin kasashe na Afirka. (Bello Wang)

Bello