logo

HAUSA

Kasashe da dama sun mara wa kasar Sin baya kan aikin kiyaye hakkin bil Adama

2021-09-29 14:00:00 CRI

Kasashe da dama sun mara wa kasar Sin baya kan aikin kiyaye hakkin bil Adama_fororder_210929-k01-许多国家在联合国人权理事会发声支持中国

Kasashe 65 sun gabatar da jawabin hadin kai a ranar 24 da 27 ga wata a yayin taron hukumar kare harkokin hakkin bil Adama ta MDD karo na 48 don mara wa kasar Sin baya, baya haka, kasashe 20 sun yi jawabi bi da bi, inda suka jinjinawa nasarorin da Sin ta samu a fannin kiyaye hakkin bil Adama, tare da yin kira da a girmama ikon mulkin kasar Sin da cikakkun yankunanta, baya ga nuna adawa kan yadda ake tsoma baki cikin batutuwan Xinjiang da Hong Kong da Tibet da sauran harkokin cikin gidan kasar Sin.

Kasashen Afirka ta kudu da Cote d’Ivoire da Ghana da Mali da wasu kasashe 11 sun bayyana cewa, girmama ikon mulkin kasa da ’yancin kai da cikakkun yankunan kasa da ma daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida, ita ce babbar ka’idar raya dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa. Batutuwan Xinjiang da Hong Kong da Tibet harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kasashen waje su daina tsoma baki a cikin su. Haka kuma kasashen sun mutunta manufar ”Kasar daya tak a duniya, da tsarin mulki biyu” da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa a yankin Hong Kong.

A nata bangare, kasar Ghana ta nuna rashin amincewa kan yadda aka siyasantar da batun hakkin dan Adam, da ma lahanta ci gaban harkokin hakkin dan Adam na sauran kasashe ta hanyar tsoma baki a harkokin cikin gidansu bisa bambancin ma’auni. A nata bangare, kasar Ruwanda ta nuna adawa da yadda wasu kasashe ke tsoma baki a batutuwan da suka shafi yankunan Xinjiang da Hong Kong na kasar Sin. (Kande Gao)