logo

HAUSA

Rarraba allurar rigakafi ya bankado munafuncin kare hakkin dan adam a Amurka da kasashen Yamma

2021-09-29 20:54:58 CRI

Rarraba allurar rigakafi ya bankado munafuncin kare hakkin dan adam a Amurka da kasashen Yamma_fororder_allura

Jiya ne wakilin kasar Sin ya yi jawabi na hadin gwiwa a madadin kasashe masu tasowa sama da 30 a yayin taro na 48 na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, inda ya yi kira da a tabbatar da adalci wajen rarraba allurar rigakafi a duniya. Wannan tamkar mayar da martani ne ga "gibin rigakafin" wanda al'ummomin duniya ke nuna damuwa a kai.

Tun bayan barkewar annobar COVID-19, Amurka da wasu kasashen yammacin duniya, sun fifita son kai na siyasa sama da rayuwar dan adam da lafiyar su, inda gaba daya suka kauce daga manufar 'yancin dan adam.

A hirar da ya yi da kafafen yada labarai na Amurka, shugaban bankin raya kasashen Afirka Adesina, ya fito karara yana bayyana cewa, kasashen yammacin duniya sun nuna yaudara wajen sayar da allurar rigakafin annobar COVID-19, ba wai kawai allurar ba ta isa kan lokaci ba, amma adadin da farashin ba su dace ba.

Lokacin da 'yan siyasar Amurka da na yammacin Turai ke amfani da alluran rigakafi a matysayin wani makami na siyasa, ita kuma kasar Sin, tana yin duk mai yiyuwa don ba da allurar rigakafi ga al'ummomin kasa da kasa tare da habaka haɗin gwiwar yaki da cutar a duniya. A halin yanzu, kasar Sin ta samar da allurai biliyan 1.2 ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 100.

Alluran rigakafi wani ma'auni ne, ana iya ganin wanda ke da hakkin kare ‘yancin dan adam, haka nan ana iya kokarin gano wanda ke take haƙƙin ɗan adam. (Ibrahim)