logo

HAUSA

MDD ta bukaci bangarorin kasar Sudan su cimma matsaya guda

2021-09-29 10:00:54 CRI

MDD ta bukaci bangarorin kasar Sudan su cimma matsaya guda_fororder_210929-UN mission chief urges Sudanese parties to reach consensus-f03

Shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan, Volker Perthes, ya bukaci dukkan bangarorin kasar Sudan, su cimma matsaya guda, kana su hada hannu wajen aiwatar da ayyukan da ya kamata a yi a lokacin gwamnatin wucin gadi.

Sanarwar da gwamnatin riko ta kasar ta fitar, ta ce shugaban gwamnatin Abdel Fattah Al-Burhan ya gana da Volker Perthes ne jiya Talata a birnin Khartoum.

Sanarwar ta ruwaito Volker Perthes na cewa, samun ci gaba a gwamnatin na bukatar hadin gwiwa da tattaunawa tsakanin dukkan bangarori, ciki har da sojoji da fararen hula da dukkan kungiyoyi, ciki har da masu dauke da makamai, domin cimma ayyukan da ake fatan a yi a wa’adin shugabancin riko na kasar. (Fa’iza Mustapha)