logo

HAUSA

Sin ta taimakawa zaman lafiya da ci gaban duniya da cikakkun tsare tsaren ta

2021-09-28 21:22:56 CRI

Sin ta taimakawa zaman lafiya da ci gaban duniya da cikakkun tsare tsaren ta_fororder_wadata

A yau Talata ne gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani mai taken "Cikakkun tsare tsaren raya al’ummar kasar Sin", wadda ta yi bita game da hanyoyin da kasar ta bi, da matakan da ta aiwatar, wajen gina al’umma mai nagarta daga dukkanin fannoni.

Takardar ta bayyana cewa, Sin ta taimakawa kasashe masu tasowa da dama da hanyoyin zamanantar da al’amura. Kaza lika manufar Sin ta gina al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkanin fannoni, na kara bunkasa, ta yadda kasar ke kara dinkewa, da cudanya da sauran sassan duniya, wanda hakan ya yi matukar ingiza ci gaban duniya baki daya.

Har ila yau, takardar ta nuna cewa, al’ummar Sin za ta ci gaba da aiki tukuru karkashin jagorancin JKS, kana za ta fadada dinkewa da sauran sassan duniya.  (Saminu)