logo

HAUSA

Yankin Hong Kong ya sake tabbatar da damammaki maras iyaka ga masu saka jari na duniya

2021-09-28 10:59:52 CRI

Yankin Hong Kong ya sake tabbatar da damammaki maras iyaka ga masu saka jari na duniya_fororder_210928-Hong Kong-Ibrahim

Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong jiya Litinin ya fitar da rahoto kan yanayin kasuwanci a yankin. Inda ya nuna kyakkyawan yanayin kasuwanci da makoma mai haske ga ci gaban yankin, bayan sauyawa daga hargitsin tafiyar da harkokin mulki. Wannan shi ne rahoton yanayin kasuwanci na farko da aka fitar, tun bayan dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin. Rahoton mai shafuka 74 "fa'idodi na musamman da damar da ba ta da iyaka" sun takaita muhimmancin yanayin kasuwancin Hong Kong. A watanni shida na farkon wannan shekarar, tattalin arzikin Hong Kong ya sake farfadowa da kashi 7.8 cikin 100, kuma yawan marasa aikin yi ya ragu daga kashi 7.2 cikin 100 zuwa kaso 4.7. Tattalin arzikin Hong Kong ya dawo kamar yadda yake. Dangane da “sabbin alkaluman cibiyar hada-hadar kudi ta duniya" da aka fitar, ya nuna cewa, yanayin kasuwancin yankin Hong Kong, ya dawo a matsayin manyan uku na farko a duniya. Bayanai sun tabbatar da cewa yanayin kasuwancin Hong Kong a halin yanzu, yana da aminci kuma cike da ƙarfi.

A cikin shekarar da ta gabata ko makamancin haka, kamfanonin kasashen waje sun ci gaba da bunkasa a cikin Hong Kong.

Sakamakon yadda ake ci gaba da inganta tsarin gudanar da mulki na "Kasa Daya, Tsarin mulki iri Biyu" yankin musamman na Hong Kong zai ci gaba da kiyaye yanayin kasuwanci mai tsaro da dorewa na dogon lokaci, tare da baiwa masu saka hannun jari na kasa da kasa wadataccen sararin ci gaba. (Ibrahim Yaya)