logo

HAUSA

Jami'in diflomasiyya: Mutane a fadin kasar Sin suna more hakkoki da mutunci fiye da da

2021-09-28 11:16:13 CRI

Jami'in diflomasiyya: Mutane a fadin kasar Sin suna more hakkoki da mutunci fiye da da_fororder_210928-People across China enjoying rights and dignity as never before-i02

Minista a tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Jiang Yingfeng, ya fada wa taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD (UNHRC) karo na 48 cewa, jama’a a duk fadin kasar Sin, ciki har da Xinjiang, Hong Kong da Tibet, suna gudanar da rayuwarsu cikin aminci da gamsuwa , da more hakkoki da mutuncinsu ba kamar a baya ba.

Da yake amfani da ’yanci wajen ba da amsa a zaman hukumar na ranar Litinin, Jiang Yingfeng, ya yi nuni da cewa, wasu kasashe da kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) suna ta yada jita-jita da karya, a hannu guda kuma zargin da Amurka ke yi kan kasar Sin musamman sun fallasa cikakken yunkurinta na dakile wasu kasashe ta hanyar fakewa da hujjar hakkin dan adam.

Jami’in na kasar Sin ya kuma yi tambayar cewa, yawan ’yan kabilar Uygur a Xinjiang ya karu daga miliyan 8.34 a shekarar 2000 zuwa miliyan 11.62 a shekarar 2020, karuwar kusan kashi 40 cikin dari. To shin wannan kisan gilla ne?

Ya ce, “Amurka ta damu ne kawai, saboda ba za ta taba samun damar tsara 'juyin juya hali’ a Hongkong ta hanyar ’yan amshin shatanta ba.” (Ibrahim Yaya)