logo

HAUSA

Daidaiton Jinsi Na Nufin Ba Mata ’Yancin Samun Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Ayyukan Yi Kamar Takwarorinsu Maza

2021-09-28 16:52:01 CRI

Daidaiton Jinsi Na Nufin Ba Mata ’Yancin Samun Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Ayyukan Yi Kamar Takwarorinsu Maza_fororder_微信图片_20210928164316

BY CRI HAUSA

Da safiyar yau ne kasar Sin ta fitar da shirinta na raya harkokin da suka shafi mata da yara cikin shekaru 10 masu zuwa, wadanda za su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufar daidaiton jinsi da bayar da fifiko ga harkokin da suka shafi yara da bude wani sabon babi ga ci gaban matan da yara.

Kokarin kasar Sin na raya harkokin mata tare da tabbatar da ganin sun samu ’yanci iri guda da takwarorinsu maza a kowane bangare, zai kara nunawa duniya irin gudunmuwar da mata za su iya bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa da ake muradi.

Daidaiton jinsi ba ya nufin wai mata da maza su zama daidai, abun da yake nufi shi ne, mata da maza su samu ’yanci daidai da juna ba tare da ba wani jinsi fifiko ba. Ko shakka babu, wannan shiri na kasar Sin, zai kai ga tabbatar da zuwa shekarar 2030 an cimma hakan. Ingantuwar damarmakin mata da ’yancinsu a muhimman bangarori kamar na samun ilimi da kiwon lafiya da siyasa da tattalin arziki da ayyukan yi, abu ne da ake matukar bukata a duniya ganin yadda aka bar su a baya. Kana wannan dabara ta Sin za ta farkar da duniya daga baccin da ta yi a wannan fage.

Hakika manufofin na kasar Sin sun zama abun koyi ba kadai ga kasashe masu tasowa ba, har ma da kasashe masu karfin tattalin arziki, ganin yadda kokarinta wajen samar da damarmaki ga mata suka taimaka mata a lokacin da take yaki da talauci, inda aka ga yadda mata Sinawa suka tashi tsaye suka yi gwagwarmaya tare da bada gagarumar gudunmawa wajen fatattakar talauci.  

A kowace al’umma a duniya, an sani cewa mata da yara su ne mafi rauni, mafi fuskantar hadari wadanada kuma suke jin radadin duk wata matsala da al’umma za ta gamu da ita, don haka karfafa musu gwiwa da inganta hakkokinsu, abu ne da ya zama wajibi, ta yadda za su iya dogaro da kansu. Mata da yara na da dimbin gudunmawar da za su bayar ga ci gaban al’umma da dorewar zaman lafiya, wato mata a matsayinsu na iyaye, su kuma yara a matsayinsu na manyan gobe.

Bayan kasancewarsa tubalin tabbatar da hakkin dan Adam, daidaiton jinsi tubali ne na gina zaman lafiya da ci gaban al’umma mai dorewa.