logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da tsare-tsaren raya harokin mata da yara

2021-09-28 11:29:44 CRI

Kasar Sin ta fitar da tsare-tsaren raya harokin mata da yara_fororder_210928-China outlines development of women-f02

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta gabatar da tsare-tsaren raya harkokin da suka shafi mata da yara nan da shekaru 10 masu zuwa.

Tsare-tsaren, wadanda suka zayyana burika da ayyukan raya harkokin mata da yara da ake son cimmawa nan da shekaru 10 masu zuwa, za su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufar daidaiton jinsi da bayar da fifiko ga harkokin da suka shafi yara da bude wani sabon babi ga ci gaban mata da yara.

Bisa tsare-tsaren tabbatar da ci gaban harkokin mata a kasar Sin daga shekarar 2021 zuwa 2030, za a tabbatar da manufar daidaiton jinsi ta kowacce fuska, inda mata za su samu hidimomin kiwon lafiya da ’yancin samun ilimi da ’yancin da ya shafi tattalin arziki da muradunsu da ’yancin shiga harkokin siyasa, daidai da takwarorinsu maza.

Har ila yau, kawo shekarar 2030, dokoki da ka’idoji har ma da manufofin kare hakkokin yara za su ingantu, yayin da gibin dake tsakanin ci gaban yara a yankunan birane da karkara da yankuna daban-daban da rukunoni zai ragu sosai. Inda yara za su more damar samun daidaiton hidimomi da ayyuka na yau da kullum da kuma karin jin dadin rayuwa, wadanda za su kunshi kowa da kowa. (Fa’iza Mustapha)