logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da matsakaicin wadata

2021-09-28 13:36:21 CRI

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da matsakaicin wadata_fororder_210928-China issues white paper on moderate prosperity-i04

Talatar nan ne, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani, don yin bayani kan yadda kasar ta kai ga cimma nasarar gina al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowane fanni, ko Xiaokang.

Takardar mai taken "Fadi tashin kasar Sin daga talauci zuwa wadata," ta bayyana cewa, tabbatar da wadataccen wadata ta kowane fanni, kamar yadda aka ayyana a watan Yuli, alama ce mai matukar muhimmanci ta farfado ga kasar.

Takardar ta kuma yaba da aiki tukuru da JKS da jama'ar Sinawa suka yi, sannan ta kalli abin da kasar Sin ta cimma wajen tabbatar da wadata ta hanyar samar da ci gaba ga kowa da kowa.

Dangane da tabbatar da wadatacciyar wadata ta kowane fanni a matsayin babbar gudummawar da Sin ta ba duniya, takardar ta kuma yi bayanin yadda duniya za ta ci gajiyar ci gaban kasar Sin.

A matsayinta na kasa mafi yawan jama'a, kana babbar kasa mai tasowa a duniya, kasar Sin ta ba da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya ta hanyar samun matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni.

Bisa ga nasarar cimma al'umma mai matsakaicin wadata, kasar Sin ta taimaka matuka wajen rage yawan mutanen da ke fama da talauci a duniya tare da samun sabbin gogewa na zamanantar da bil Adam, yayin da shirinta na bude kofa ya inganta hadin gwiwar samun nasarar moriyar juna. (Ibrahim)