logo

HAUSA

An bude sabon babin hadin gwiwar fasahohin sararin samaniya

2021-09-28 13:10:27 CRI

An bude sabon babin hadin gwiwar fasahohin sararin samaniya_fororder_hoto

Yau Talata, aka kaddamar da bikin baje kolin fasahohin sararin samaniya na kasa da kasa na kasar Sin karo na 13 a birnin Zhuhai na lardin Guangdong. Yayin taron dandalin tattaunawar Zhuhai na shekarar 2021 da aka yi a jiya, wakilai daga bangarori daban daban sun nuna fatan karfafa mu’amala da hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin kan fannonin fasahohin sararin samaniya da jiragen sama, domin habaka hadin gwiwar kasa da kasa kan ayyukan da abin ya shafa.

Shugaban kamfanin Thales na kasar Faransa dake kasar Sin Jerome Bendell ya bayyana cewa,“Bunkasuwar fasahohin jiragen sama na kasar Sin ta burge ni sosai, musamman ma a fannin fasahar sararin samaniya, kamar aikin binciken duniyar Wata, da aikin sauka a duniyar Mars, kasar Sin ta taka mihimmiyar rawa a fannin raya fasahohin sararin samaniya. Kuma, muna jin dadi sosai dangane da yadda kamfanonin jiragen sama da kamfanonin kasuwanci masu nasaba da fasahar sararin samaniya suke bunkasa a kasuwannin kasar Sin, kana, za mu ci gaba da nuna goyon baya domin raya kasuwannin da abin ya shafa.” (Maryam)