logo

HAUSA

Kasar Sin ta lashi takobin ganin yarjejeniyar CTBT ta fara aiki

2021-09-28 10:38:23 CRI

Kasar Sin ta lashi takobin ganin yarjejeniyar CTBT ta fara aiki_fororder_210928-china-f01

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya yi alkawarin kasar Sin za ta ci gaba da kokarin bada gudummawar ganin yarjejeniyar haramta gwajin makaman nukiliya ta CTBT ta fara aiki.

Zhang Jun ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar cewa, yarjejeniyar na da muhimmanci ga yunkurin da ake na kawar da makaman nukiliya daga duniya. Kuma a nata bangaren, kasar Sin na bada gudunmawa wajen ganin yarjejeniyar ta fara aiki, ta fuskar shirye-shiryen aiwatar da ita da kuma hadin gwiwar kasa da kasa. Ya ce yana mai jaddada cewa, Sin ba za ta kawo tsaiko ga aikin yarjejeniyar ba.

Ya kara da cewa, ba tare da la’akari da yanayin siyasar duniya ba, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye tsarin huldar kasa da kasa da tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kare tsarin kwance damarar makaman nukiliya da yaduwarsu. Haka zalika, Sin za ta ci gaba da hada hannu da sauran bangarori wajen ci gaba da bayar da gudunmawa ga matsayar da kasashen duniya suka cimma na haramta gwajin makaman nukiliya da ganin an aiwatar da yarjejeniyar tare da dagewa wajen ganin an cimma burin haramtawa da lalata makaman nukiliya baki daya nan bada jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)