logo

HAUSA

Kitchen na Kauna

2021-09-27 13:00:00 CRI

Kitchen na Kauna_fororder_Wan Zuocheng and Xiong Gengxiang1

Akwai wani kitchen na musamman a wani loko kusa da asibitin cutar daji na Jiangxi dake Nanchang, babban birnin Lardin Jiangxi dake gabashin Kasar Sin. A lokacin cin abinci sau 3 a kowacce rana, ‘yan uwan marasa lafiya dake asibitin kan yi amfani da kitchen din wajen dafa abinci ko kunu ko romo, domin kai wa marasa lafiya. Wasu miji da mata, Wan Zuochen da Xiong Gengxiang ne ke tafiyar da kitchen din tsawon shekaru 18. Su ne ke samar da risho da kayayyakin girki ga mutanen a kan farashi mai rahusa, wato kudin Sin Yuan 1, kwatankwacin centi 15 na Amurka, domin dafa abinci guda.

Asali dai, Kitchen din ya kasance wajen sayar da karin kumallo da Wan da Xiong ke tafiyar da shi. Su kan soya fanke mai dadi, kuma ya yi fice a unguwar. Su kan samu odar karin kumallo daga asibitin.

Wata rana a shekarar 2003, da wasu ma’aurata suka wuce shagon na Wan da Xiong, Sai suka hango har a lokacin murhu na ci, duk da cewa Wang da Xiong sun kammala soya fankensu. Sai ma’auratan suka nemi su yi amfani da murhun domin dafawa dansu abinci. Dan nasu yaro ne matashi dake fama da cutar dajin kashi. Yaron yana son cin abincin da mahaifiyarsa ta dafa yayin da yake kwance a asibiti. Wan da Xiong sun kyale matar nan ta dafa abinci a kyauta.

Daga nan, sai Wan da Xiong suka fara bayar da kayayyakin kitchen din domin mutane su yi amfani da su kyauta su dafawa marasa lafiya abinci. Yayin da labarin ya bazu, sai mutane suka fara kiran wurin da “kitchen na asibitin cutar daji” ko kuma “Kitchen na Kauna” wanda ke sa zukatansu da kuma cikinsu jin dadi.

Wan da Xiong ba su taba nadamar ba mutane wannan dama ba. “iyalan marasa lafiya sun fi mu shan wahala” cewar Xiong. Baya ga kula da harkokinta na kasuwanci, a shirye Xiong take ta saurari labaran gwagwarmayar iyalan marasa lafiya. Ta yi ammana sauraronsu, zai rage musu damuwa.

Domin baiwa karin mutane damar girki a lokaci guda, dole Wan da Xiong suka sayi karin kayayyaki suka kuma fadada shagon fanken zuwa babban kitchen. Mutanen da suka yi amfani da kitchen din kan dage sai sun biya kudi, ciki har da kudin ruwa da na makamashi da sauran kayayyakin girki. A don haka ne Wan da Xiong suka sanya farashi: Yuan 1 na amfani da kitchen domin dafa abinci ko kuma sayen kunshin shinkafa, sai yuan 2.5 na dafa romo. Ba sa karbar kudin ruwa da na sinadaran dandano. Yayin da komai kyauta ne ga marasa karfi.

Kitchen na Kauna_fororder_Wan Zuocheng and Xiong Gengxiang3

A hankali a hankali, Wan da Xiong dake tunkarar shekaru 70, sun shafe shekaru 18 suna tafiyar da wannan kitchen. Su kan tashi da karfe 4 na asubahin kowacce rana domin shirya kitchen din. Su kan tafasa ruwa tare da dafa shinkafa, ta yadda mutane kan zo su yi amfani da kitchen din cikin sauki. “kada ku sanya damuwa a ranku. Ku tabbata kun ci abinci mai kyau,” haka Xiong kan fadawa iyalan marasa lafiya. Xiong da mijinta sun saba kasancewa cikin aiki tun daga asuba har maraice. Ba su da lokacin dafa na su abincin har sai bayan 9 na dare.

Daga safiya har zuwa dare, kusan kullum za a samu murhun wannan kitchen na kauna yana ci. Domin saukakawa mutane amfani da kitchen din, Wan da Xiong na tsaftace shi, su share tare da yin wanke-wanke. ‘ya’yan ma’auratan sun dade suna son iyayen nasu su huta, su rufe kitchen din na wasu kwanaki, su tafi wani wuri su huta. Amma iyayen sun ki.

Wasu lokuta, Wan ba ya jin dadi saboda ya san aikin a kullum na da wahala, amma matarsa na ba shi goyon baya tare da taimaka masa tafiyar da kitchen din. Xiong kan cewa mijinta, “abu mafi farin ciki shi ne, tafiyar da kitchen din da taimakawa mutane”.

Ko a mawuyacin lokacin yaki da annobar COVID-19 a kasar Sin, Wan da Xiong sun bar kitchen din a bude ga iyalan marasa lafiya. Domin tabbatar da ana bayar da tazara da rage hadarin yaduwar cutar, ma’auratan ba sa barin mutane na shiga. A maimakon haka, su kan karbi kayayyakin girki daga masu aikin sa kai, inda daya daga cikinsu zai wanke tare da shirya kayayyakin girki, yayin da dayan zai dafa abinci. Idan suka gama, sai su ba masu aikin sa kan su kai wa ‘yan uwan marasa lafiyan.

Kitchen na Kauna_fororder_Wan Zuocheng and Xiong Gengxiang2

Tun bayan sanin marasa lafiya da ‘yan uwansu, Wan da Xiong, sun kara fahimtar wahalhalun da mutane ke sha. Sun kuma gano cewa, abincin da aka dafa a gida zai karawa marasa lafiya sinadaran gina jiki da karfin yakar cutar daji.

Galibin iyalan marasa lafiya kan rubuta lambobin wayarsu a jikin bangon kitchen din. Iyalan marasa lafiya kan yaba da taimakon da Wan da Xiong ke ba su, kuma da dama daga cikinsu sun gayyace su domin su ziyarci gidajensu. Kitchen din na sanya marasa lafiya da iyalansu jin tamkar suna gida. Wan da Xiong na ajiye da wani littafi a kitchen din, kuma galibin iyalan marasa lafiya kan rubuta kalmomin fatan alkhairi ga ma’auratan a cikin littafin. Ma’auratan sun gamsu da kafa kitchen din, a ganinsu, yana taimakawa wajen ba mutane kwarin gwiwar yaki da cutar daji.

A bara, gwamnatin birnin Nanchang, ta samar da kudi ga Wan da Xiong domin bunkasa kitchen din. Ma’auratan kuma sun gyara shi, suka sa tayil da rumfa mai kare ruwan sama da kayayyakin kashe gobara. Gwamnatin ta kuma samar masu tallafi domin taimaka musu biyan kudin haya.

Wan da Xiong na daga cikin mutanen da aka yi wa lakabi da masu “tafiyar da kasar Sin gaba” a 2020. A lokacin da aka gudanar da bikin bayar da lambar yabon a birnin Beijing, a watan Fabrairun bana, Wan da Xiong ba su halarta ba, domin suna fargabar iyalan marasa lafiya ba za su samu damar amfani da kitchen din ba idan suka yi tafiya. A ganinsu, kitchen din na kawo farin ciki da kwanciyar hankali ga marasa lafiya, wadanda tamkar suna fagen daga. “idan wani ya shiga hali mafi kunci a rayuwa, idan kuma wani zai iya taimaka masa samun sauki, to mai taimakawar ma zai samu farin ciki”, cewar Wan.

Wan da Xiong na da da namiji guda da ‘ya’ya mata biyu. Su kan jaddada muhimmanci kulawa da mutane ga ‘ya’yansu. “duk yawan kudin da za ku yi, kada ku manta da taimakawa masu bukata,” sun sha nanatawa ‘ya’yansu hakan.

Yayin da ma’auratan ke ci gaba da tsufa, wasu mutane kan tambaye su, yaushe suke shirin rufe kitchen din su yi murabus. Su kan dage cewa, za su ci gaba da tafiyar da shi muddun suna da karfin yin hakan.(Kande Gao)

Kande