logo

HAUSA

Habasha za ta rufe ofishin jakadancinta dake Cairo

2021-09-27 10:22:27 CRI

Habasha za ta rufe ofishin jakadancinta dake Cairo_fororder_0927Ethiopia-Fa'iza

Jakadan Habasha a Masar, Markos Tekle Rike, ya ce kasarsa za ta dakatar da ayyukan ofishin jakadancinta na Masar har na tsawon watanni 3 zuwa watanni 6 daga watan Oktoba, saboda dalilai na tattalin arziki.

A cewar rahoton kafar yada labarai ta Arham, jakadan ya bayyana cewa, matakin ba shi da nasaba da takkadamar dake tsakanin Habasha da Masar da Sudan kan katafariyar madatsar ruwan Habashar.

Ya kara da cewa, kwamishinan ofishin Jakadancin zai ci gaba da tafiyar da harkokin ofishin na tsawon lokacin dakatarwar.

A baya-bayan nan, Habasha ta rufe ofisoshin jakadancinta a kasashe da dama saboda matsalolin tattalin arziki da take fuskanta. (Fa’iza Mustapha)