CAETE 2021: Faduwa Ce Ta Zo Daidai Da Zama
2021-09-27 17:12:05 CRI
BY CRI HAUSA
Yayin da tattalin arzikin kasashen duniya ke kara fuskantar matsin lamba sakamakon barkewar annobar COVID-19, zamu iya cewa, tamkar abin nan ne da masu hikimar magana ke cewa, “kaya ya tsinke a gindin kaba”, a wani kaulin kuma, “abin nema ne ya samu wai matar makadi ta haifi ganga.” A daidai lokacin da annobar COVID-19 ke kara karya lagon tattalin arzikin duniyar, zamu iya cewa, bikin baje kolin raya tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayya na Sin da kasashen Afrika wanda aka bude a wannan mako zai taimakawa sassan biyu wajen rage radadin matsin tattalin arzikin ga bangarorn biyu, musamman ma ga nahiyar Afrika wajen samun farfadowa daga matsalolin da annobar ta haifar ga tattalin arzikinsu. A ranar 26 ga wata ne aka kaddamar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka wato CAETE, a karo na biyu a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin. Bikin na daga cikin manyan matakai takwas da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar a wajen taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2018 wanda aka gudanar a Beijing babban birnin kasar Sin, kuma a bisa yadda aka tsara, za a dinga gudanar da bikin na CAETE ne a duk bayan shekaru biyu, kuma wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da wannan muhimmin biki, wanda kuma zai gudana tsakanin ranar 26 zuwa 29 ga watan Satumbar shekarar 2021. A wannan karo, za a mai da hankali ne kan hadin gwiwar sassan biyu a fannonin abinci, da amfanin gona, da kiwon lafiya, da manyan ababen more rayuwa, da hada-hadar kudi da sauransu. An kiyasta kamfanoni kusan 900 ne suka halarci bikin na wannan karo, ciki har da wadanda suka zo daga kasashen Afirka kusan 40. Bikin zai nuna nasarorin da Sin da Afirka suka cimma bisa hadin gwiwarsu, tare da baje kolin kayayyakin da kasashen Afirka suka samar, kuma za a yi amfani da bikin wajen kara inganta hadin gwiwar sassan biyu. Hakika za mu iya cewa tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama, domin kuwa bikin baje kolin na wannan karo ya zo ne a dai dai lokacin da bangarorin biyu suka fi matukar bukatar hadin gwiwa da juna domin yin aiki tare wajen samun farfadowar daga kodamar tattalin arzikin dake damun kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa, kuma Afrika tana cikin yanayi na neman farfadowa daga tasirin annobar ta COVID-19 wacce ta kasance babbar barazana ga tattallin arziki da zaman rayuwar al’ummar duniya masamman kasashe marasa karfi. Ko shakka babu, baje kolin CAETE tamkar wata dama ce ta neman cike babban gibin tattalin arzikin da zaman rayuwar al’ummun Sin da Afrika. (Ahmad Fagam)