Shirin raya karkarar Sin ya ingiza bunkasuwar noma da kawata karkara da bunkasa arzikin manoma
2021-09-26 16:06:03 CMG
“Noma na da matukar wahala, amma yana matukar faranta zaciyata."
Wani manomi Kong Puzhong, ya fadawa manema labarai a wajen bikin ranar girbi ta manoman kasar Sin wanda aka gudanar kwanan nan a yankin Changsha, na lardin Hunan.
Iyalan Kong Puzhong, suna noma wata gonar iyali a yankin Liuyang, dake lardin Hunan, a shiyyar kudancin tsakiyar kasar Sin. A cewarsa, shinkafar da iyalinsa ke nomawa ana sayar da kowane kilo guda akan yuan 30 a kasuwa. Koda yake tana da tsada, sai dai tana da matukar farin jini a wajen masu sayanta. Ya ce shinkafar tana da inganci matuka, kuma ba su yin amfani da maganin kashe kwari da takin zamani wajen nomanta.
Kong Puzhong ya ce, an samu yabanya mai yawa a wannan shekarar. An rore shinkafa mai nauyin kilo kusan 50,000 a gonarsa, kuma jimillar kudin shigar da aka samu ya zarce miliyan 2. Duk wadannan an same su ne saboda amfani da tsarin noma na zamani wanda gwamnatin ta bullo da su. Idan an kwatanta da tsarin da suke amfani da shi a shekarun baya, iyalansa sun samu kudin shigar da ya rubanya sama da sau uku..
Kong Puzhong daya ne daga cikin daruruwan miliyoyin manoman kasar Sin da suka samu gagarumar yabanya a kakar bana.
A halin dake ake ciki yanzu a kasar Sin, daruruwan miliyoyin kananan manoma suna aiki tukuru domin samun farin ciki, da kuma yadda tsarin aikin gonar ke kara samun karfi, da kawata yankunan karkara, kana yadda manoma ke kara yin arziki ya tabbata a zahiri.(Ahmad)