logo

HAUSA

Shen Haixiong: Masu amfani da yanar gizo da suka jinjinawa dawowar Meng Wanzhou gida Sin sun zarta kwatankwacin al’ummun Amurka da Canada

2021-09-26 16:00:07 CRI

Shen Haixiong: Masu amfani da yanar gizo da suka jinjinawa dawowar Meng Wanzhou gida Sin sun zarta kwatankwacin al’ummun Amurka da Canada_fororder_shen haixiong

Yau Lahadi da safe, mataimakin ministan ma’aikatar yada manufofin kasar Sin kuma shugaban CMG Shen Haixiong ya halarci bikin kafa asusun zuba jari kan sana’o’in kafar watsa labarai ta zamani ta CCTV da aka shirya a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin, inda ya fayyace cewa, shirin kai tsaye da CCTV ya gabatar game da dawowar madam Meng Wanzhou gida kasar Sin daga kasar Canada ya jawo hankalin masu amfani da yanar gizo a fadin kasar matuka, har adadinsu wadanda suka jinjinawa lamarin ya kai miliyan 400, adadin da ya zarta kwatankwacin al’ummun kasashen Amurka da Canada.

Shen Haixiong ya bayyana cewa, “Lamarin ya nuna cewa, al’ummun Sinawa suna jiran dawowar madam Meng gida, haka kuma ya nunawa al’ummun kasa da kasa karfin al’ummun Sinawa.”

Shen ya kara da cewa, dawowarta gida ya nuna manufar rike mulki ta mayar da moriyar al’ummun kasa a gaban kome ta JKS, haka kuma ya shaida cewa, jagorancin JKS da kasar Sin mai karfi, goyon baya mai karfi ne na al’ummun kasar Sin wadanda adadinsu ya kai biliyan 1.4.(Jamila)