logo

HAUSA

An sake tonuwa karairayin kasashen yamma game da Xinjiang da yadda suke yaudarar duniya

2021-09-26 21:02:08 CRI

An sake tonuwa karairayin kasashen yamma game da Xinjiang da yadda suke yaudarar duniya_fororder_xinjiang

A ranar 26 ga watan nan na Satumba, gwamnatin kasar Sin ta fidda takardar bayani mai taken “Karuwar adadin al’ummar Xinjiang", takardar wacce ta yi bayani filla-filla tare da cikakkun alkaluma, kana ta nunawa duniya kyakkyawan misalin kasar Sin, da yadda kabilun kasar ke yin hadin kai da juna, wajen samar da ingantaccen ci gaban kananan kabilun kasar.

Alkaluman shekarar 2020 sun nuna cewa, a shekaru 10 da suka shude, saurin karuwar al’ummar yankin Xinjiang yana mataki na hudu a kasar, kuma karuwar adadin al’ummar yankin ya kai mataki na 8 a kasar. A hannu guda kuma, yawan ‘yan kabilar Uyghur ya ci gaba da karuwa a bisa matsayin koli, inda ya karu daga adadin mutane 8,345,600 a shekarar 2000 zuwa adadin mutane 11,624,300 a shekarar 2020, wato a kowace shekara adadin na karuwa da kashi 1.67%. Bugu da kari, takardar bayanin ta kuma fayyace cewa, yawan al’ummar Xinjiang, musamman ‘yan kananan kabilu, zai ci gaba da karuwa sannu a hankali nan da wasu lokuta masu zuwa. Kamar ka yi tambaya ne cewa, shi ko kasar dake samun karuwar jama’a tana da wani abin da ya shafe ta game da batun “kisan kare dangi"?

Ban da wannan kuma, kamar yadda alkaluman yawan karuwar jama’a ya nuna wato (HDI), matakin karuwar al’ummun kananan kabilun yankin Xinjiang ya samu gagarumin ci gaba ta fuskar matakin tsawon ran al’umma, da matakin ba da ilmi, da kuma ingancin rayuwa.

Alkaluman kididdiga sun tabbatar cewa, ci gaban karuwar al’ummar yankin Xinjiang ya kai matsayin da ba za a iya kwantan shi ba a tarihin shekarun aruruwa da suka gabata. Karairayi da kasashen yamma ke yadawa masu nasaba da batun yankin Xinjiang manufa ce ta nuna adawa da ci gaban kasar Sin, wanda ba zai taba yaudarar kasashen duniya ba, kuma ba zai taba yin tasiri wajen hana bunkasuwar kasar Sin da kuma ci gaban kasar ba. (Ahmad)