logo

HAUSA

Manoman kasar Sin sun gudanar da shagulgulan murnar samun girbi mai armashi

2021-09-24 21:47:02 CRI

Manoman kasar Sin sun gudanar da shagulgulan murnar samun girbi mai armashi_fororder_微信图片_20210924214549

Noma tushen tattalin arziki, kamar yadda bahaushe kan ce.

A kwanan nan ne, Sinawa a sassa daban daban na kasar suka gudanar da shagulgula na murnar bikin girbi na manoma, bikin da ya fado a jiya Alhamis, ranar 23 ga wata.

Manoman kasar Sin sun gudanar da shagulgulan murnar samun girbi mai armashi_fororder_微信图片_20210924214557

A nan kasar Sin, an ayyana kafa bikin girbi na manoma ne a shekarar 2018, inda aka tsai da kudurin gudanar da bikin a yanayin kaka, lokacin da tsawon rana ke daidai da dare, wato wanda ya kan fado a tsakanin ranar 22 zuwa 24 ga wata, kuma a wannan shekara, an gudanar da bikin ne a jiya 23 ga wata, wato a karo na 4.

Walikiyarmu Lubabatu ta kuma kawo mana tsaraba daga lardin Hunan da ke tsakiyar kasar, inda aka gudanar da kasaitaccen biki.