logo

HAUSA

Masar za ta kaddamar da kashi na biyu na aikin samar da riga-kafin kamfanin Sinovac nan da makonni 5

2021-09-24 10:56:57 CRI

Masar za ta kaddamar da kashi na biyu na aikin samar da riga-kafin kamfanin Sinovac nan da makonni 5_fororder_210924-Ahmad2-Masar

Kasar Masar za ta kaddamar da kashi na biyu na aikin samar da riga-kafin COVID-19 na kamfanin kasar Sin Sinovac nan da makonni biyar, kamar yadda ministar lafiyar kasar Hala Zayed, ta bayyana.

Zayed, ta bayyana cikin jawabin da ta gabatar a taron manema labarai na haidn gwiwa tare da jakadan kasar Jamus dake kasar Masar Frank Hartmann, a birnin Alkahira cewa, tuni sun riga sun karbo kayayyakin aikin da masana’antu ke bukata domin hada alluran riga-kafin guda miliyan 15, kuma a yanzu haka suna karba karin wasu kayan hada alluran riga-kafin guda miliyan 15.

A ranar 18 ga waran Yuli, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Masar Sameh Shoukry, sun halarci bikin kaddamar da fara aikin samar da riga-kafin cutar COVID-19 na hadin gwiwa kimanin allurai miliyan 1 a kasar Masar, wacce ita ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta yi hadin gwiwa da kasar Sin don samar da riga-kafin cutar ta COVID-19.

Zayed ta ce, a halin yanzu cibiyoyin suna iya samar da alluran riga-kafin guda miliyan biyu a kowane mako karkashin hadin gwiwar kamfanin kasar Masar VACSERA, da na kasar Sin Sinovac, inda ta bayyana cewa Masar tana burin samar da alluran riga-kafin guda miliyan 80 ya zuwa karshen watan Disambar wannan shekara. (Ahmad)