logo

HAUSA

Cutar Kwalara ta yi sanadin mutuwar mutane 329 a arewacin Nijeriya

2021-09-23 11:17:16 CRI

Cutar Kwalara ta yi sanadin mutuwar mutane 329 a arewacin Nijeriya_fororder_0923F2-Najeriya

Barkewar cutar kwalara a jihar Kano, ta yi sanadin mutuwar a kalla mutane 329 tun daga watan Maris.

Yayin wani taron manema labarai game da barkewar cutar, Sulaiman Iliyasu, jami’in dake sa ido kan barkewar cututtuka a jihar, ya ce ana zargin mutane 11,475 sun kamu da cutar a  fadin kananan hukumomin jihar 44 tun daga watan Maris da ta gabata.

A cewarsa, daga cikin wancan adadin, 11,115 sun warke, yayin da 329 suka mutu. Yana mai cewa, zuwa ranar Talata, 31 daga cikinsu na jinya a yankunan kananan hukumomin jihar 3. (Fa’iza Mustapha)