logo

HAUSA

Yarjejeniyar AUKUS Za Ta Saba Doka Da Odar Kasa Da Kasa

2021-09-23 16:26:18 CRI

Yarjejeniyar AUKUS Za Ta Saba Doka Da Odar Kasa Da Kasa_fororder_src=http___inews.gtimg.com_newsapp_bt_0_13999446836_641&refer=http___inews.gtimg

Daga Amina Xu

Amurka da Birtaniya da Austriliya sun sanar da kafa kungiyar AUKUS a yayin wani taro, aikin dake gabanta shi ne taimakawa Austriliya wajen kafa wata rundunar jiragen karkashin teku da ke aiki da makamashin nukiliya. Matakin da ba shakka zai saba tsarin doka da odar kasa da kasa.

Da farko dai, kasashe biyar masu kujerun dindindin a majalisar dinkin duniya ne kawai ke da jirgin karkashin teku dake aiki da makamashin nukiliya don kiyaye zaman lafiya da karkon duniya. Ganin yadda na’urar da ake amfani da ita a jirgin na iya sarrafa makaman nukiliya, don haka tsaronta na da alaka matuka da zaman lafiyar shiyya-shiyya da na kasa da kasa. Idan wata kasa ta sayar da fasahar jirgin ga sauran kasashe, lamarin zai haddasa illa ga tsaron nukiliya, kuma ya sabawa yarjejeniyar hana yaduwar nukiliya da aka kulla. Yarjejeniyar ta yi tanadin cewa, bai dace kasashen da suka mallaki nukiliya su sayar da makaman nukiliya ko na’urorin nukiliya ga sauran kasashe ba, kuma ba a yarda wadannan kasashe su taimakawa saura wajen kera makaman nukiliya ba. Ko da yake jirgin ba mai dauke da hakikanin bam ko kuma abubuwan fashewa na nukiliya ba ne, amma saboda halinsa na da alaka da makaman nukiliya, hakan ya sa yana karkashin wannan yarjejeniya. Wannan yarjejeniyar ta tanadi cewa, idan wata kasa ban da wadannan kasashe biyar suna son su mallaki makaman nukiliya, za a yi mata hukunci mai tsanani. Idan sauran kasashe sun koyi yadda Amurka ta yi sun sayar da fasahar jirgin ga saura, to kasashe da dama za su mallaki jirgin, wadanda za su jibge karkashin teku a wurare daban daban, abin da zai kawo babbar baranaza ga zaman lafiyar duniya. Ranar 26 ga watan Satumba ranar kawar da makaman nukilya ce, don haka yanke wannan shawarar ta kafa AUKUS da kasashen Amurka da Birtaniya da Australiya suka yi, a daidai wannan lokaci, ya bata ran jama’ar duniya baki daya. Kiyaye tsaron nukiliya na bukatar hadin kan kasa da kasa, ko wata babbar kasa ma ya kamata ta sauke nauyin dake wuyanta don kiyaye zaman doka da odar duniya a maimakon keta su bisa son kai.

Na biyu, yarjejeniyar AUKUS ta keta yarjejeniyar da Faransa da Austriliya suka kulla a baya. Shekarar 2016, kasashen biyu sun kulla wata yarjejeniya ta kudin Euro biliyan 56, inda Austirliya na shirin sayen wasu jiragen karkashin ruwa guda 12 daga hannun Faransa. Amma, AUKUS na shirin taimakawa Austriliya wajen kafa wata rundunar jirage karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya, abin da ya sa Austriliya ta yi watsi da kwangilar da ta kulla da Faransa. Mataki ya kasance yin takara ba bisa doka ba, kuma Austriliya ta yi watsi da amanarta ta zama inuwa guda da wasu don cimma moriyarsu. Idan sauran kasashe sun koyi abin da take yi sun ci amanar abokansu, to ba wanda zai nace ga yarjejeniya, kuma zaman oda da doka na duniya ya tashi a banza, har za a tada yake-yake tsakanin kasashe daban daban.

Ban da wannan kuma, Amurka da Birtaniya da Austriliya sun taba bayyana cewa, matakin da AUKUS ke dauka na nufin tinkarar kasar Sin. A matsayin hannun Amurka wajen takara da kasar Sin ko da yaushe, Austriliya bata da isashen karfi a wannan fanni saboda yadda take da nisa sosai da kasar Sin, amma yanzu Austriliya za ta mallaki irin wadannan jirage masu amfani da makamashin nukiliya, abubuwan da za su kasance kamar idanu dake karkashin ruwa, wadanda za su kawo barazana ga Sin har ma duk shiyyar Asiya-Pacific.

A karshe, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labarai cewa, karamar kungiya wadda ta sabawa muradun wannan karni da keta muradun shiyya-shiyya da na kasa da kasa, kowa zai yi adawa da ita, kuma ba za ta cimma nasara ba ko kadan, abin da ya zama martani da Sin take yi game da matakin da AUKUS ke dauka na keta zaman oda da dokar duniya. (Amina Xu)