logo

HAUSA

Har Kullum Kasar Sin Na Martaba Gudummawar Manoma A Matsayin Su Na Muhimmin Jigon Raya Kasa

2021-09-23 16:42:37 CRI

Har Kullum Kasar Sin Na Martaba Gudummawar Manoma A Matsayin Su Na Muhimmin Jigon Raya Kasa_fororder_0923-01

A ’yan kwanakin baya, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke rangadi a lardin Shaanxi, ya ware lokaci musamman domin ganawa da manoman kauyen Gaoxigou na gundumar Mizhi. A lokacin tattaunawa da manoman, shugaba Xi ya jinjina musu, tare da karfafa gwiwar su bisa muhimmiyar gudummawar da suke baiwa ci gaban kasa.

A kuma tsakiyar wannan mako, yayin da ake bikin girbi na manoman kasar, shugaban na Sin ya sake mika sakon gaisuwa ga daukacin mutanen dake aiki a fannin noma da raya karkara.

Cikin kalaman shugaba Xi, har kullum ana iya tuna yadda ya sha nanata cewa, ba za a taba mantawa da gudummawar manoma ba, kuma ba za a taba watsi da yankunan karkara ba. Irin wadannan kalamai na karfafa gwiwa, da yaba gudummawar manoman kasar Sin, ko shakka babu suna kara nuni ga muhimmancin da gwamnati da jama’ar kasar Sin ke dorawa ga sha’anin noma, kasancewarsa jigo na raya tattalin arzikin kasar tun daga tushe.

Bisa mahangar gwamnatin kasar Sin, gudummawar sana’ar noma ba ta tsaya ga samar da isasshen abinci ga miliyoyin al’ummar kasar kadai ba, kasancewarta wani muhimmin ginshiki na gaggauta ayyukan yaki da fatara, da zamanantar da cin gajiyar amfanin gona, baya ga taimako da hakan ke bayarwa ga kara inganta rayuwar manoma, da rage gibin da ke akwai tsakanin birane da yankunan karkara.

Ko shakka babu, kasar Sin ta ciri tuta a fannin noma, ta kuma ci dimbin gajiya daga alfanunsa, a fannin farfado da yankunan kasar baki daya.

Shaidu na zahiri sun tabbatar da cewa, yayin da kasar Sin ke tunkarar sabuwar alkibla ta cimma muradun karni na gaba, ko shakka babu, ba za ta bar fannin noma, da inganta rayuwar manoma, da raya karkara a baya ba. (Saminu Alhassan)