logo

HAUSA

Kwallon kafa ta lokacin hutu na baiwa matasan ‘yan kwallo a Kamaru damar kaiwa ga burin su na shiga manyan gasanni

2021-09-23 19:20:22 CRI

Kwallon kafa ta lokacin hutu na baiwa matasan ‘yan kwallo a Kamaru damar kaiwa ga burin su na shiga manyan gasanni_fororder_0923-wasanni

A birnin Yaounde na kasar Kamaru, lokacin hutun ‘yan makaranta muhimmin lokaci ne da akan ga yara da matasa na sassan kasar daban daban, na ta buga tamaula a filaye masu kura, ana iya ganin yara matasa sanye da riguna kala kala, suna buga kwallo yayin da ‘yan kallo ke shewa.

Cikin su, Hamza Abdouraman matashi ne dake bayyana burin sa na zama shahararren dan kwallo, wanda zai nunawa duniya kwarewarsa. Duk da cewa yana so da farko ya yi suna a Kamaru, a hannu guda yana fatan kaiwa ga nahiyar turai, kana yana fatan taka leda a kungiyar Manchester United.

Matashin mai shekaru 26 da haihuwa na cikin yara ‘yan Kamaru masu dinbin yawa, dake fatan yin suna tare da samun arziki ta hanyar taka leda. A lokacin da irin wadannan matasa ke na su kwazon, akwai kuma manajoji, da koci koci dake farautar matasan ‘yan wasa masu basira a kasar

Kungiyar kwallon kafar da Abdouraman ke takawa wasa, wato “Money FC, na buga wata gasa da ake shiryawa a lokacin hutun ‘yan makaranta, lokacin da wakilin Xinhua ya isa filin wasan da suke buga kwallo.

A cewar Mouhamadou Aminou, mashiryin gasar, akwai kyaututtuka masu maiko da za a baiwa ‘yan wasan da suka zamo zakaru a gasar. Akwai kuma tanadin gabatar da su ga manyan kulaflika domin su buga wasa a kungiyoyin kwararru, inda daga nan za su iya tsallakawa zuwa manyan kulaflika har da na waje.

Manyan ‘yan wasa masu buga irin wannan gasa ta lokacin hutun ‘yan makaranta a baya, a yanzu su ne ke daukar nauyin shirya gasar, domin samar da damar horo da kwarewa ga ‘yan baya tun suna kanana.

A Kamauru kwallon kafa tamkar addini take, don haka mutane irin su Aminou ke shirya gasanni lokacin da yara ke hutu a ko wace shekara, wadda kan baiwa yara har na kauyuka damar shiga a dama da su, lamarin da ke zama wata dama har a birane ta samun nishadi.

A Kamaru, yara na matukar kaunar wannan gasa, a wasu lokuta akan ga yara ba ko takalmi, daga iyalai daban daban, daga kabilu, da mahangar siyasa daban daban suna wasan kwallo tare.

Wasu daga irin wadannan yara ‘ya’yan talakawa ne, wadanda ke da burin cimma manyan nasarori a rayuwa ta hanyar kwallo kafa, da fatan hakan zai ba su zarafin taimakawa iyalan su fita daga kangin talauci.

Idan an dubi tarihi, za a ga cewa, wasu daga shahararrun ‘yan kwallo ciki har da dan wasan da ya taba zama mafi hazaka a nahiyar Afirka har karo 4 wato Samuel Eto'o, da kuma dan wasa mafi hazaka a Afirka cikin shekaru sama da 50 wato Roger Milla, dukkanin su sun fara ne da taka leda a irin wadannan gasanni na lokacin hutun ‘yan makaranta, a kananan filayen dake cike da kura, wasun su ba tare da takalmi a kafafunsu ba.

Bisa shirin hukumar kwallon kafar Afirka AFCON, kasar Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafar nahiyar da za a buga a badi. Don haka ga yara masu burin cimma manyan nasarori a fannin kwallon kafa, gasar ta hukumar AFCON tana yi musu kaimi, duba da cewa a gasar mai zuwa, taurarin ‘yan wasan nahiyar irin su Mohamed Salah, da Sadio Mane na a Senegal za su hallara.

Don haka ne ma adadin matasan ‘yan wasa dake halartar gasar a bana ke karuwa, a cewar Louis Tangono, wanda ke horas da kungiyar Mokolo FC. Tangono ya ce "Muna lalubo yaran ‘yan kwallo dake taka leda a nan da can, wadanda kuma ba su da wata alaka da masu shirya gasar. Muna kuma fitar da kwararrun ‘yan wasa matasa daga kungiyoyin kwallon kafar birnin Yaounde.

Sai dai duk da karatowar wannan gasa, a bangaren kasar ta Kamaru, akwai babban kalubale. Duk da cewa gwamnatin kasar ta kammala ginin katafaren filin wasa na zamani, a shirin ta na karbar bakuncin gasar ta AFCON, a hannu guda, har yanzu unguwanni da yankunan al’ummu marasa galihu ne ke fitar da ‘yan kwallon kasar mafiya yin fice. To sai dai kuma idan an kwatanta da yawan wadanda ke samun cikar burin su a wannan fage, masharhanta na cewa, cikin duk kusan matasa ‘yan kwallo 500, daya kacal ke iya ketarawa har ya kai ga matsayi na bajimta.

Bugu da kari, ko da ma ‘yan kadan din da kan kai ga samun nasara, kalilan ne ke iya samun damar bugawa manyan kungiyoyi da ke biyan su makudan kudade. Amma duk da haka, matasan Kamaru ba sa watsi da burin su, da mafarki na cimma babban sakamako!