Kasar Sin na ba da muhimmanci sosai kan aikin gona da yankunan karkara da kuma manoma
2021-09-22 09:48:27 CRI
A ranar 23 ga watan nan na Satumba ne za a gudanar da bikin ranar girbi ta manoman kasar Sin, inda ake sa ran gudanar da shagulgula 3 a bikin na bana a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan, da birnin Jiaxing na lardin Zhejiang da kuma Deyang na lardin Sichuan. Kaza lika akwai karin birane da larduna 11, da za su shiga a dama da su a bikin girbin na bana.
A shekarar 2018 ne ake fara gudanar da wannan biki a hukumance, bayan da ya samu amincewa daga gwamnatin kasar Sin. Yayin bikin da zai gudana a birnin Changsha na Hunan, za a shirya bukukuwa iri daban daban, a muhimman dandaloli biyu, tare da kananan dandaloli biyu na daban a fadin lardin.
Wannan dai biki shi ne mafi girma da aka ware domin manoman kasar Sin, wanda ke da nufin karfafa gwiwar manoma, da jinjinawa kwazon su na kirkire kirkiren raya sana’ar su, da ma ba su damar musamman, ta yin murnar manyan nasarori da suka samu a fannin.
Sanin kowa ne cewa, kaso mafi tsoka na al’ummar Sinawa tun fil azal manoma ne, wadanda gudummawarsu ce ta haifar da ci gaban da kasar ta samu kawo yanzu. Kaza lika, baya ga ciyar da kasa, manoman kasar Sin sun ba da gagarumar gudummawa wajen raya yankunan karkara, ta fannin fadada harkokin tattalin arziki da zamantakewa.
A hannu guda kuma, bisa tarihi, manoman kasar Sin sun yi rawar gani wajen mara baya ga ayyukan JKS, wadanda suka hada da juyin juya hali, da gina kasa, da aiwatar da sauye sauye.
Bisa hakan ne ma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, ba za a taba watsi da manoma ba, kana ba za a taba watsi da yankunan karkara ba a kowane irin lokaci.
Bikin ranar girbi ta manoman kasar Sin, kamar ko wace shekara, a bana ma zai kunshi nuna wasannin gargajiya, da nuna kwarewa a fannin sana’ar ta noma, da kuma dandana nau’o’in abinci daga sassan yankunan kasar ta Sin daban daban. (Saminu Hassan, Ahmad Fagam/Sanusi Chen)