logo

HAUSA

Wahalar Aiki Ba A Fara Ba

2021-09-22 16:30:42 CRI

Wahalar Aiki Ba A Fara Ba_fororder_0922-01

Wahalar Aiki Ba A Fara Ba_fororder_0922-02

’Yan sama jannatin kasar Sin din nan guda 3, sun dawo doron duniya lami mafiya, a ranar 17 ga watan Satumba, bayan da suka shafe watanni 3 suna aikin ginin sashen tashar sararin samaniya mallakar kasar Sin. Wannan wani babban ci gaba ne ba kawai ga kasar Sin ba, har ma ga sauran sassan duniya, domin zai rage babakeren da wasu kasashe ke yi a fannin binciken sararin samaniya.

A wannan rana ne, bangaren kumbon dawowa doron duniya na Shenzhou-12, ya sauko yankin Dongfeng na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin, dauke da Nie Haisheng, da Liu Boming da kuma Tang Hongbo cikin nasara. Wahalar aiki ba a fara ba.

Idan ba a manta ba, a ranar 17 ga watan Yuni ne, aka harba kumbon Shenzhou-12 daga cibiyar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin Sin, inda bayan isarsa sararin samaniya, kumbon ya hadu da bangaren ma’aikata na Tianhe na tashar sararin samaniya ta Sin. Bayan tsayawarsa ne kuma ’yan sama jannatin su 3 suka shiga bangaren ma’aikata na Tianhe, inda suka fara aiki na watanni 3, aikin da ya kammala cikin nasara har suka dawo gida.

Bayan kammala wannan muhimmin aiki na tsawon watanni uku, ranar Litinin kuma kasar Sin ta sake harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-3 da yi yi jigilar wasu kayayyaki kusan ton 6 zuwa tashar sararin samaniya da take aikin ginawa. Aiki ga mai kare ka.

An yi amfani da rokar Long March-7 Y4, wajen harba kumbon Tianzhou-3, daga tashar harba tauraron dan Adam ta Wenchang dake lardin Hainan, daga bisani kumbon Tianzhou-3 zai hade da muhimmin sashe na Tianhe da kumbon Tianzhou-2 a tashar sararin samaniyar.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, a shirye ta ke ta yi hadin gwiwa da dukkan kasashe dake da sha’awa a fannin binciken sararin samaniya. Wannan ya kara nuna kudirin kasar Sin na hadin gwiwa da samun nasara tare da ma yadda take sauke nauyin dake bisa wuyanta a fannin binciken sararin samaniya da kokarin gina kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. Wani albishir da mahukunta na kasar Sin suka sha bayyanawa shi ne, da zarar wannan tasha ta fara aiki, kofa a bude ta ke ga duk kasar dake sha’awar shiga a dama da ita a harkokin binciken sararin samaniya cikin lumana da bangaren kasar Sin. (Ibrahim Yaya)