Dr. Mainasara Kogo Umar: Ana bukatar kara hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka
2021-09-21 15:05:31 CRI
Barrister Dr. Mainasara Kogo Umar, lauya ne, kana shahararren mai sharhi kan harkokin yau da kullum, kuma masanin harkokin kasa da kasa ne dake birnin Abujan Najeriya.
A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Dr. Mainasara ya yi tsokaci kan dangantaka da hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, sa’annan a cewarsa, dorawa kasar Sin laifin kwace albarkatu daga Afirka, ko kuma yada jita-jita cewa wai kasar Sin ita kadai, ke cin moriya daga hadin-gwiwar ta da kasashen Afirka, ban da ita Afirka, ba daidai ba ne, kuma abu ne da bai kamata a ce haka ba. (Murtala Zhang)