logo

HAUSA

Manufofin kasar Sin sun sha bambam da na ‘yan jari hujja

2021-09-20 17:25:22 CRI

Manufofin kasar Sin sun sha bambam da na ‘yan jari hujja_fororder_0920-01

Har kullum mahukuntan kasar Sin sun sha jaddada aniyar gwamnatin kasar game da kudirinta na kyautata makomar bil adama ta bai daya ba tare da gindaya wasu sharruda ko kuma nuna amfani da karfin tuwo ko mulkin danniya ba. A lokuta da dama, jami’an gwamnatin kasar Sin suna bayyanawa duniya manufofin kasar wadanda sun yi hannun riga da na wasu kasashen ‘yan jari hujja. Alal misali, koda a karshen wannan mako, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana wasu kalamai dake kara fito da manufofin kasarsa a fili game da alakarta da kasa da kasa inda shugaban yace, Sin za ta taimaki duk wata kasa dake da bukatar kyautata rayuwar al’ummarta. Yayin da shugaban ya halarci taro karo na 21, na majalisar shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice ta kafar bidiyo daga Beijing, inda ya gabatar da muhimmin jawabi. Cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya jaddada cewa, nan da wasu shekaru 3 masu zuwa, kasarsa za ta samar da gurabe 1000 na samun horo a fannin yaki da talauci, ga kasashe membobin kungiyar SCO, za ta kuma kafa wasu ma’aikatun koyar da sana’o’i 10 masu suna “Luban Workshop” a kasashen, tare kuma da gudanar da ayyukan hadin-gwiwa guda 30, a fannonin da suka shafi kiwon lafiya, yaki da talauci, bada ilimi da raya al’adu, a wani kokari na taimakawa kasashen dake da bukatar inganta kwarewarsu, wajen tafiyar da harkokin kasa da kyautata walwalar al’umma. Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, idan ana son daidaita harkokin kasa da kasa, bai dace a yi la’akari da karfi da matsayin da wata kasa take da su ba, ko kuma nuna babakere da mulkin danniya ga sauran kasashe. Ya ce ya kamata a girmama ka’idojin kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya, da tsayawa kan yin shawarwari da more damammaki cikin hadin-gwiwa. A wani batu makamancin wannan, wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar kula da ayyukan gona da samar da abinci ta MDD, FAO, Guang Defu, yace a matsayinta na babbar mai bada taimako, mai shiga a dama da ita, kana muhimminyar kasar dake bayar da gudunmawa ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kasar Sin a shirye take tayi aiki tare da hukumomin FAO, da IFAD da WFP, da sauran kasashe mambobin MDD, wajen cike gibin cigaba a tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu sukuni, domin a samu damar cimma nasarar kawar da yunwa da talauci. Hakika, manufofin kasar Sin sun bambamta da na maru rajin bin tafarkin jari hujja.(Ahmad Fagam)