Mahmooda Taqwa Milad: Mai kiwon tumaki da ta zama malama a jami'a
2021-09-20 22:29:57 cri
Mahmooda Taqwa Milad, ta shafe kuruciyarta a wani kwari da ake kira Do Ab a jihar Vardak dake tsakiyar kasar Afghanistan. Mazauna kauyen sun yi mata lakabi da “Yarinyar da ke zuwa makaranta”.
A tsakiyar shekarun 1990, Taqwa mai shekaru 7, ta kasance tana doguwar tafiya a hanya mai duwatsu a kowace rana, don zuwa wata makarantar 'yan mata. Kullum tana cikin kadaici, saboda babu wata yarinyar dake zuwa makaranta a kauyensu. Don kawai ta zabi zuwa makaranta, mutanen kauyen sun mayar da ita saniyar ware, kuma ba su yarda 'ya'yansu mata su yi wasa da ita ba.
Taqwa ta yi karatu na tsawon shekaru biyu kacal a makarantar firamare, sai ta bar makarantar. Lokacin da Taqwa ke hira da ‘yan jaridarmu, tana zaune a kasa, ko tana tunanin ko ta yi shiru, hawaye na zuba a idanunta. Ta ce, bayan wancan lokaci sai ta tattara ganyayyaki a bakin kogi don dumama gida da dafa abinci, gami da kiwon tumaki a tsaunuka. A cewarta, ta zauna a kauyen na tsawon shekaru 9, ciki kuwa ta dauki shekaru 5 tana kiwon tumaki.
An haifi Taqwa a shekarar 1988. A wancan shekarar, Tarayyar Soviet ta janye sojojinta bayan mamaye Afghanistan na tsawon shekaru 9, daga baya sai Afghanistan ta fada cikin yakin basasa. Bisa wannan halin da ake ciki, wasu mutane sun tsere zuwa kasashen waje, wasu kuma sun buya cikin kauyuka. Mahaifinta, wanda ke koyarwa a Kabul ya rasa aikin yi, kuma babu dabara sai kawai ya gudu tare da iyalinsu zuwa garinsu da ke lardin Vardak. Taqwa ta ce, a lokacin tana karama ba ta iya tuna yawancin abubuwan da suka faru, amma abin da ya burge ta sosai, shi ne iyalinsu suna tashi da karfe 12 na dare, kuma su kan boye a cikin kogo don kada a gano su.
Taqwa ita ce yarinya mafi kankanta a cikin iyalin, tana da manyan 'yan'uwa 6 da manyan 'yan'uwa mata 3. A yayin da suke zaune a garinsu, wannan babban iyali yana dogaro ne da wata karamar gona don ci gaba da zaman rayuwarsu.
Makarantar firamare da Taqwa ke karatu tana cikin wani kauye mai nisa. Makarantar 'yan mata ce da kasashen Larabawa suka taimaka wajen ginawa, malama daya ce a makarantar, ita ke koyar da dukkan darussa. Taqwa tana tafiya na dogon lokaci ita kadai a kan hanya mai laka a kowace rana. Lokacin da take gamuwa da mazauna kauyen, su kan ce, "Ga waccan yarinyar da ke zuwa makaranta ..."
Bayan shekaru biyu tana karatu a makaranta, wata rana ambaliyar ruwa ta afku a wurin, Taqwa ta fada cikin kogi yayin da take tsallake gadar katako, sai dai ta yi sa’a dan uwanta ya cece ta. Amma, tun daga wancan lokacin, iyalinta ba su yarda ta ci gaba da zuwa makaranta ba.
A watan Oktoban shekarar 2001, Taqwa wacce take kiwon tumaki a kauyen na tsawon shekaru biyar, ta yi amfani da wata dama mai kyau, wato dan uwanta ya koma babban birnin kasar, ita ma ta koma Kabul don ci gaba da karatunta. Amma saboda shekarunta na haihuwa, sai ta nemi shiga aji bakwai kai tsaye, wato aji na farko a makarantar midil.
Ajin da Taqwa ke karatu yana da rabin rufi ne kadai, kuma akwai dalibai mata 9 a ajin. Malamin su ya taba dukan Taqwa, saboda ba ta iya yin rubutu ba kwata-kwata, sakamakon rashin ilimin asali na haruffa da nahawu. Taqwa tana kuka ta gudu zuwa gida, mahaifinta ya tambaye ta, "Ko dai kina son komawa kauye domin ki rika raka mahaifiyarki, tare da yin aikin gida?" Taqwa ta share hawayenta ta ce "A'a!"
Taqwa, wadda ke da hazaka kuma mai karfin zuciya, cikin sauri ta cimma nasara a fannin karatu. A cikin jarabawar kammala aji na 7 ta zama ta farko na ajin, a aji 11 wato ajin shekara ta biyu ta makarantar sakandare, ta samu lambar yabo ta fitacciyar daliba. A lokacin kusantowar “Jarabawar shiga jami’a”, hanyar Taqwa wajen shirya jarabawa ita ce, ta bayar da wata sanarwa cewa, ‘Yan matan da ke son yin jarabawar shiga jami’a, da fatan za ku je dakin taro ko wace safiya, kuma zan taimaka muku maimaita darussa na awa daya.
Bayan ta shiga jami’a, Taqwa ta samu maki mai kyau a fannin karatu, har ta zamo lamba one sau da yawa. Amma, bayan ta kammala karatu a jami’a, sai ta tsaida kudurin zama malama a jami’a, ta gamu da matsaloli masu yawa. Ta ce, ba sa karbar mata a matsayin malamai. Ko da wane yare ko kabila kuke magana, ba a yarda da mata. Ta yi jarrabawa har sau hudu, kafin ta cimma nasara a karo na karshe.
A yau Taqwa malama ce a Jami'ar Kabul, inda ta riga ta samu digiri na biyu, tana koyar da yare da adabi na Pashto. Tana koyar da daliban aji guda uku a ko wace rana, ko wane aji dake da dalibai a kalla 50. Tana amsa ko wace tambaya daga dalibai ta hanyar amfani da manhajar hira. Ko da yake ta kasance mai shan aiki, ta yadda har ba ta iya amsa sakon sauran mutane, amma tabbas sai ta amsa sakon dalibanta. Tana daukar dalibanta kamar abokanta, kuma ko da yaushe tana kokarin taimaka wa dalibai mata.