logo

HAUSA

CMG zai kasance kafar watsa labaru daya tilo da zai yi amfani da Sinanci wajen watsa labaru game da bikin baje kolin duniya na Dubai

2021-09-20 20:37:08 CRI

CMG zai kasance kafar watsa labaru daya tilo da zai yi amfani da Sinanci wajen watsa labaru game da bikin baje kolin duniya na Dubai_fororder_0920-02

A yau ne, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya sa hannu kan yarjejeniya tare da kamfanin kula da bikin baje koli na duniya na shekarar 2020 na Dubai, don haka CMG zai kasance kafar watsa labaru daya tilo mai amfani da Sinanci don watsa labaru game da bikin baje kolin duniya na Dubai.

Da farko, an tsai da shirin gudanar da bikin baje koli na duniya na Dubai ne a shekarar 2020, wato tsakanin ranekun 20 ga watan Oktoba na shekarar ta 2020 zuwa 10 ga watan Afrilun shekarar 2021. To sai dai kuma sakamakon tinkarar cutar COVID-19, ya sa aka dage gudanar da bikin zuwa ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2021 zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022.

Wannan ne karon farko da aka gudanar da bikin a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma ya zuwa yanzu kasashe 192 sun tabbatar da halartar bikin. (Zainab)