logo

HAUSA

A waiwayen shirin ayyukan CPPCC da shugaba Xi Jinping ya gabatar don duba sabon ci gaban ayyukan majalisar

2021-09-19 17:30:00 CRI

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC hukumar musamman ce da aka yi shawarwari bisa demokuradiyya da tsarin gurguzu. A yayin cika shekaru 70 da kafa majalisar CPPCC a shekarar 2019, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yaba da shirin ayyukan majalisar CPPCC a sabon lokaci a dukkan fannoni, inda ya jaddada cewa, ya kamata a inganta ayyukan yin shawarwari kan harkokin siyasa, da sa ido bisa demokuradiyya, da shiga aikin siyasa da ba da shawarwari kan aikin siyasa, ta hakan za a kara fahimtar juna da cimma daidaito don kiyaye tsarin majalisar CPPCC da raya tsarin yadda ya kamata.

A watan Agusta na bana, majalisar CPPCC ta gudanar da taron manema labaru kan manyan batutuwan da ake kula game da aikin sa kaimi ga raya yankin yammacin kasar Sin da samun bunkasuwa mai inganci. Wannan shi ne kirkire-kirkiren da aka yi a tsarin majalisar CPPCC karo na 13, ya zuwa yanzu, an riga an gudanar da irin taro sau 27, burinta shi ne taimakawa membobin majalisar da su gano yanayin ayyukan siyasa da samar da sharadi gare su don gudanar da ayyukansu. Farfesa a kwalejin kula da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa ta jami’ar Renmin ta kasar Sin kuma direktar cibiyar nazarin jam’iyyun Sin da na kasashen waje ta Zhejiang dake birnin Jiaxing Zhou Shuzhen tana ganin cewa, wannan mataki zai taimakawa membobin majalisar CPPCC wajen gudanar da aikinsu na shiga harkokin siyasa yadda ya kamata. Ta ce,

“Gudanar da irin wannan taro kan manyan batutuwa bisa manyan tsare-tsaren jam’iyyarmu da kasarmu, zai taimakawa membobin majalisar CPPCC wajen gudanar da ayyukansu na ba da shawara kan harkokin siyasa yadda ya kamata, membobin za su gano dalilin da ya sa aka haifar da matsaloli da hakikanin yanayin batun, ta hakan za su tsara hanyoyi masu dacewa don warware matsalolin, ta yadda za su taka rawarsu a matsayin membobin majalisar mai amfani.” (Zainab)