Issoufou Kalidou Abdoulkarim: Ina jin dadin karatu da rayuwa a kasar Sin!
2021-09-18 19:55:11 CRI
Issoufou Kalidou Abdoulkarim, wani dan Jamhuriyar Nijar ne wanda ke karatun digiri na uku a halin yanzu a jami’ar koyon aikin gona ta kasar Sin dake Beijing. Malam Abdoulkarim wanda ya yi shekaru uku yana karatu da rayuwa a kasar Sin, ya ce ya kulla zumunta da mutanen kasar Sin da dama, musamman malamai da abokan karatu a makaranta, har ma ya ce ta hanyar zurfafa karatu a nan, ya samu karin ilimi sosai a harkar aikin gona. A karshe malam Issoufou Kalidou Abdoulkarim ya yi kira ga matasan Afirka su kudiri aniyar yin wani abu, daga baya su jajirce don cimma burinsu. (Murtala Zhang)