Shawarwarin Sin sun kafa alkibla ga daidaita matsalar Afghanistan yadda ya kamata
2021-09-18 20:55:43 CRI
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen taron koli kan batun kasar Afghanistan na hadin-gwiwar shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO da na kungiyar CSTO, inda ya fitar da wasu muhimman shawarwari dangane da daidaita matsalar Afghanistan ta hanyar siyasa, ciki har da taimakawa ga wanzar da zaman lafiya a kasar ba tare da wani jinkiri ba, da kaddamar da tattaunawa da mu’amala da kasar, tare kuma da taimakawa al’ummar kasar haye wahalhalun da suke fuskanta yanzu. Shawarwarin suna da babbar ma’ana da taka rawar gani wajen shimfida zaman lafiya da sake gina Afghanistan, har ma da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a wannan shiyya.
Kasar Afghanistan wadda ta sha fama da fadace-fadace tana kan wata muhimmiyar gaba. A matsayin ta na makwabciyar kasar, Sin na fatan hada hannu da kasashe membobin kungiyoyin SCO da CSTO, don marawa al’ummar Afghanistan baya wajen neman makoma mai haske, da tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar. (Murtala Zhang)