logo

HAUSA

Wakilan ECOWAS sun isa birnin Conakry

2021-09-18 15:22:09 CRI

Wakilan ECOWAS sun isa birnin Conakry_fororder_ECOWAS

Tawagar wakilan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), dake karkashin jagorancin shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, sun isa birnin Conakry, fadar mulkin kasar Guinea a jiya.

Tagawar za ta gana da shugabannin gwamnatin soja na kasar Guinea, inda za su sanar da kudurin da shugabannin kungiyar ECOWAS suka cimma a yayin taron da suka yi a kasar Ghana a ranar Alhamis. Kuma, za su kara kakkaba wa gwamnatin sojan da ta kai yujin mulki takunkumi, kamar rike kudade da kadarorinsu da na iyalansu da sauransu. (Maryam)