logo

HAUSA

Shawarar kasar Sin za ta taimaka ga bude sabon babi ga ci gaban kungiyar SCO

2021-09-18 20:51:07 CRI

Shawarar kasar Sin za ta taimaka ga bude sabon babi ga ci gaban kungiyar SCO_fororder_A

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi ta kafar bidiyo a wajen taro na 21 na majalisar shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice wanda aka yi jiya Jumma’a, inda a cewarsa, ya dace a kara gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin kasashe membobin kungiyar SCO, da bayar da karin gudummawa ga wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a duk fadin duniya.

Shugaba Xi ya kuma yi kira a kara tallata “ruhin Shanghai”, da bayar da wasu muhimman shawarwari guda biyar game da ci gaban kungiyar SCO a nan gaba, tare kuma da sanar da wasu sabbin manyan matakan da kasar sa za ta dauka. Kasa da kasa na ganin cewa, jawabin Xi zai taimaka sosai ga bude sabon shafi ga bunkasar kungiyar SCO, da shimfida dauwamammen zaman lafiya da wadata a duk duniya.

Shawarwari guda biyar da shugaba Xi ya bullo da su sun hada da, kama hanyar inganta hadin-gwiwa, da kama hanyar jin dadi da fuskantar hadari tare, da kama hanyar bude kofa ga kasashen waje da kara mu’amala da koyi da juna, da kuma kama hanyar shimfida adalci. Shawarwarin ba kafa alkibla ga ci gaban kungiyar SCO a nan gaba kawai suka yi ba, har ma da nuna cewa, kasar Sin kasa ce dake daukar nauyin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samar da wadata a duk duniya.

A nasa bangaren, shehun malami Tursunali Kuziev daga jami’ar koyon aikin jarida da ilimin watsa labarai ta kasar Uzbekistan ya ce, shawarwari biyar da shugaba Xi Jinping ya bullo da su, na da babbar ma’ana ga kara gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin kasashe membobin kungiyar SCO, kana, shiri gami da matakan kasar Sin sun sanya sabon kuzari ga ci gaban kungiyar. (Murtala Zhang)