logo

HAUSA

An ayyana karshen cutar Marburg a kasar Guinea

2021-09-17 09:50:03 CRI

An ayyana karshen cutar Marburg a kasar Guinea_fororder_210917-fa'iza-3-Marberg virus

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce kasar Guinea ta ayyana kawo karshen cutar Marburg a jiya Alhamis, bayan shafe kwanaki 42 ba tare da samun sabon wanda ya kamu da cutar ba a kasar.

Wata sanarwa da ofishin WHO na Afrika, wanda ke Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Congo ya fitar, ta ce hukumomin lafiya na Guinea, da taimakon WHO, sun gaggauta daukar dabarun da suka hada da kai daukin gaggawa da tura kwararru domin gudanar da karin bincike da inganta sa ido kan yaduwar cutar da tantance hadarinta da kara wayar da kan al’umma da gwaji da jinya tare kuma da daukar matakan kandagarki da dakile cutar.  (Fa’iza Mustapha)