logo

HAUSA

Yadda Sinawa suke murnar bikin tsakar lokacin kaka

2021-09-17 20:08:43 CMG

Yadda Sinawa suke murnar bikin tsakar lokacin kaka_fororder_c

Bayan wasu kwanaki za a  yi bikin tsakiyar lokacin kaka a nan kasar Sin. Saboda da haka, a yau bari ku saurari bayanin da zan gabatar muku dangane da wannan biki.

Ran 15 ga watan Agusta bisa kalandar gargajiyar Kasar Sin ita ce ranar bikin tsakiyar lokacin kaka, ko kuma mu ce Mid-Autumn Day a Turance. A wannan rana da dare wata ya fi da'ira. Ya zama cikakke, tamkar ba wanda ya raba shi. Sabo da haka an ba wannan rana ma’anar musamman ta “babu rabuwa”, da samun “cikakken iyali”. Inda mambobin iyali su kan taru a wannan rana, don taya juna murnar bikin tare. (Bello Wang)

Bello