Wakilin Sin: ’yancin ci gaban dan adam a duniya ya gaza kaiwa matakin da ake tsammani
2021-09-17 14:18:18 CRI
’Yancin cigaban bil adama batu ne da kowa ya amince da shi ba tare da jayayya ba, to sai dai kuma, a halin da ake ciki a yanzu, yanayin ’yancin ci gaban ya yi matukar gaza kaiwa kan matakin da ake tsammani, kamar yadda babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin ya bayyana.
Yayin gabatar da sanarwar hadin gwiwa a madadin kasashen duniya sama da 50 a wajen taron kolin hukumar kare hakkin dan adam ta MDD karo na 48 a ranar Alhamis, Chen Xu, wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, ya bukaci hukumomin kare hakkin dan adam na MDD da su ba da fifiko ga batun ci gaban bil Adama kuma a sanya shi cikin muhimman tsare-tsaren MDDr. (Ahmad Fagam)