logo

HAUSA

Watakila Amurka za ta yaudari Birtaniya da Australiya

2021-09-17 20:56:39 CRI

Watakila Amurka za ta yaudari Birtaniya da Australiya_fororder_A

Da ma kasar Faransa ta yi shirin gudanar da bikin murnar cika shekaru 240 da kaddamar da yakin Chesapeake a teku tare da kasar Amurka a yau Jumma’a 17 ga wata. A shekaru 240 da suka wuce, yakin da aka kaddamar a mashigin teku na Chesapeake, muhimmin bangare ne cikin yakin kwatar ‘yanci daga turawa ‘yan mulkin mallaka na Amurka. Sakamakon katse hanyar samar da guzuri a teku ta sojojin Birtaniya da sojojin Faransa suka yi, sojojin Birtaniya ta mika wuya ga sojojin hadin-gwiwar Amurka da Faransa a karshe, har ma Amurka ta samu ‘yanci.

Amma a ranar jiya 16 ga wata, kasashe uku ciki har da Amurka da Birtaniya da Australiya, sun sanar da kafa kawancen tsaro na yankin Indiya da tekun Pasifik mai suna Aukus, da daddale yarjejeniyar morewa, gami da kera jiragen karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya, da nufin nuna ja-in-ja da kasar Sin, abun da ya sa aka yi watsi da yarjejeniyar kera jiragen karkashin ruwan mai kunshe da zunzurutun kudade da aka daddale tsakanin Faransa da Australiya, hakan ya janyo matukar takaicin Faransa har ta soke bikin murnar da ta yi shirin gudanarwa.

Watakila Amurka za ta yaudari Birtaniya da Australiya_fororder_B

Abun da ya kamata Birtaniya da Australiya suke maida hankali a kai shi ne, ko sun cancanta su taimaki Amurka wadda ke cin amana gami da yaudarar kasashe kawayenta sau da yawa. A matsayin ta na kasar dake mallakar makaman nukiliya, Amurka ta hada kai tare da Birtaniya don baiwa Australiya da ba sa da makaman nukiliya taimakon raya fasahohin makaman nukiliya masu amfanin soja, lamarin da zai haifar da babbar illa ga daidaita batun nukiliyar zirin Koriya ta Arewa da na Iran, har ma da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya baki daya.

Tsohon shugaban majalisar nahiyar Turai Donald Tusk, ya taba yin gargadin cewa, in akwai aminiyar kasa irin Amurka, wa zai bukaci makiyi? In Birtaniya da Australiya sun manta da haka, babu shakka za su fuskanci babbar matsala a nan gaba. (Murtala Zhang)