Akwai hadin-gwiwa mai dorewa tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN
2021-09-16 21:02:30 CRI
Memba a majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar aiki a wasu kasashe makwabta hudu, musamman ziyarar da ya yi a wasu kasashen dake kudu maso gabashin Asiya, ciki har da Vietnam, da Kambodiya, da Singapore, ziyara ce da ta jawo hankali sosai, wadda ta nuna cewa, hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN na da dorewa, da kwarewa sosai wajen shawo kan mummunan tasiri, da illolin da sauran wasu kasashe suka haifar.
Abun lura shi ne, a ‘yan shekarun nan, Amurka ta kara karkata hankalinta kan yankin Asiya da na tekun Pasifik, da nufin taka birki ga ci gaban kasar Sin. Kwanan nan ministan tsaron Amurka, da mataimakiyar shugaban kasar sun ziyarci Singapore, da Vietnam, da sauran wasu kasashen dake kudu maso gabashin Asiya, inda suka kara gishiri kan batutuwan da suka ce wai kasar Sin barazana ce. A daidai wannan lokaci, ministan harkokin wajen Sin ma ya ziyarci Vietnam, da Kambodiya gami da Singapore, abun da a cewar kafofin yada labaran kasashen yamma, takara ce ta fannin siyasa da aka kaddamar tsakanin Sin da Amurka.
Irin wannan ra’ayin, rashin fahimta ne da aka yi game da ziyarar ministan wajen kasar Sin a wannan karo. Bana ne ake cika shekaru 30 da kafa dangantakar yin shawarwari tsakanin Sin da kungiyar ASEAN, shekara ce mai ma’anar musamman ga bangarorin biyu. Kana ziyarar minista Wang Yi ta bayyana sahihin fatan kasar Sin, na fadada hadin-gwiwa tare da kasashen dake kudu maso gabashin Asiya wajen yakar cutar COVID-19 da zurfafa hadin-gwiwar su.
Hasali ma dai, kasashen kungiyar ASEAN sun cimma ra’ayi daya cewa, daidaita dangantakar su da wasu manyan kasashe ta hanyar da ta dace, don kada su zama tamkar makami da sauran wasu kasashe ke amfani da shi, shi ne zabin da ya yi daidai, kana mafi dacewa da moriyarsu a wannan yanki. Alal misali, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam Nguyễn Phú Trọng ya jaddada cewa, babu wanda zai iya girgirzawa, gami da sauya hadin-gwiwar da ake yi tsakanin Vietnam da kasar Sin. Shi ma ministan harkokin wajen Singapore Vivian Balakrishnan ya bayyana cewa, kasarsa na fatan Sin da Amurka za su iya daidaita takarar su yadda ya kamata, da neman moriya, da nasara tare da kasashen dake wannan yanki. (Murtala Zhang)