logo

HAUSA

Har yanzu kasar Sin jigo ce ga ci gaban tattalin arzikin duniya

2021-09-16 10:31:48 CRI

Har yanzu kasar Sin jigo ce ga ci gaban tattalin arzikin duniya_fororder_210916-ruiping-Ahmad

Mahukuntan kasar Sin sun fidda bayanan tattalin arzikin kasar na watan Agusta a ranar 15 ga wannan wata, inda bayanan suka nuna cewa, alkaluman wasu muhimman fannonin kasar Sin a watan na Agusta suna cikin yanayi mai kyau, kudaden biyan hakkokin ma’aikata suna cikin daidaitaccen yanayi, tattalin arzikin kasar yana cigaba da farfadowa, kana saurin bunkasuwar kasar na ci gaba da bayyana a fili. A lokaci guda kuma, ana ci gaba da aiwatar da sauye sauye da daga matsayin tsarin tattalin arzikin kasar, kana ana ci gaba da bullo da dabarun da za su kyautata ci gaban kasar, da kara yin amfani da managartan tsare tsaren farfado da tattalin arzikin kasar Sin, da kuma daga matsayin daidaita ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.

Tilas ne a yabawa matakin bullo da muhimman manufofin bunkasa tattalin arzikin kasar da ci gaba da inganta muhallin kasuwanci, da yadda aka samu saurin karuwar kamfanonin kirkire kirkire a kasuwannin kasar Sin. Fasahar kirkire kirkire tamkar wani sashe ne wanda ba a iya kai karshensa, wanda ya taimaka matuka wajen daga matsayin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.

Kamar dai kamfanin BlackRock, daya daga cikin kamfanoni masu kula da harkokin zuba jari mafi girma a duniya, a kwanan nan ya fidda alkaluman zuba jari na duniya na tsakiyar shekarar 2021, ya ce idan an kwatanta da sauran kasashen duniya, tattalin arzikin kasar Sin ya yi matukar bunkasuwa gami da jure mummunan tasirin da annoba ta haifar ga tattalin arzikin duniya kuma ya zama tamkar shi ne ke jagorancin tattalin arzikin duniya. Ya zama babban ginshikin bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Ahmad)