logo

HAUSA

Tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da jurewa kalubale

2021-09-16 18:40:47 cri

Tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da jurewa kalubale_fororder_saminu

Masharhanta da dama na ci gaba da jinjinawa karkon da tattalin arzikin kasar Sin ya nuna, wanda a baya bayan nan ya jure kalubale masu yawa, ciki har da bazuwar cutar numfashi ta COVID-19, wanda ya haifar da takaituwar tafiye-tafiye, da zirga-zirgar masu yawon shakatawa, da ma bala’in ambaliyar ruwa da wasu sassan kasar suka fuskanta. Dukkanin wadannan sun shaida karfi, da nagartar tsare-tsaren da aka gina tattalin arzikin kasar a kan su.

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, Sin ta zamo zakaran gwajin dafi tsakanin kasashe masu tasowa, bisa yadda ta yi nasarar kawar da kangin talauci tsakanin al’ummunta, da ma yadda take kara kyautata manufofin raya kasa, da inganta rayukan al’ummarta.

A watannin baya bayan nan, Sin ta samu bunkasuwa a fannonin sarrafa hajojin masana’antu, da ribar da masana’antun ke samu, yayin da masana’antun sarrafa manyan hajojin fasahohin zamanin kasar ke kara samun tagomashi.

Bugu da kari, fannin hada hadar sayayya a cikin kasar ya samu ci gaba, kana fannin samar da karin guraben ayyukan yi a birane shi ma na kara fadada bisa daidaito.

Yayin da al’ummar kasar Sin ke ci gaba da amfana daga managartan matakan raya tattalin arzikin kasa bisa adalci, a hannu guda kuma, gwamnatin kasar na kara bullo da karin matakai, na karfafa farfadowar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

Bisa wadannan alkaluma da shaidu na zahiri, ana iya cewa, kasar Sin ta ciri tuta, a fannin raya tattalin arziki, duk da kalubale daban daban dake fuskantar ta a gida, da ma tasirin koma bayan tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)