Hadin Kan Sin Da Afrika Mai Cin Moriya Tare Abin Da Afirka Ke Bukata
2021-09-15 18:41:49 CRI
Daga Amina Xu
Shafin yanar gizon jaridar “Punch” ta Najeriya ya ba da labari cewa, shugaban Congo Kinshasa Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo ya yi kira da a sake bincike kan kwangilar hakar ma’adinai da tsohon shugaban kasarsa ya kulla tare da kasar Sin a shekarar 2008, yana mai fatan a yi ciniki bisa adalci. Shugaba ya gabatar da tunanin jawo hankalin masu zuba jari na ketare a watan Maris na bana, ba da dadewa ba kamfanin Barrick mai hakar zinari na Canada ya bayyana cewa, shugaban na da burin hadin kai da su, wannan kamfani yana gudanar da harkoki awurin hakar zinari na Kibali dake kasar ta Congo, daya daga cikin wurare mafi girma 10 a duniya na hakar zinari. Shugaban ya nemi a yi bincike kan kwangilar bayan ya gana da shugabannin kamfanonin Barrick da Glencore da nufin cewa, mai yiwuwa akwai rashin adalci tsakanin hadin kan kasashen biyu. Matsayin da shugaba ya dauka na da alaka da matakin da wasu kasashen yamma ke dauka na shafawa Sin bakin fenti.
A hakika dai, matakan da wasu kasashen yamma su kan dauka don bata hadin kan Sin da Afrika su ne wai Sin ta tabka magudi wajen baiwa kasashen Afrika rancen kudi da kwace albarkatun Afrika, shafin yanar gizon jaridar Morning Star ta Birtaniya ya ruwaito darektanshirin nazarin Sin da Afrika na kwalejin harkokin kasa da kasa na jam’iyar Johns Hopkins Deborah Brautigam na cewa, a nahiyar Afrika da ke da mutane miliyan 600 ke fama dakarancin wutar lantarki, an yi amfani da 40% na rancen kudin da Sin take bayarwa wajen samar da wutar lantarki, sauran 30% an yi amfani da su wajen zamanintar da manyan ababen more rayuwa ta fuskar zirga-zirga wadanda suke da koma baya sosai. Ban da wannan kuma, tawagarmadam Deborah Brautigam ta yi nazari cewa, rancen kudin da Sin take baiwa Afrika na bisa farashin kudin ruwa maras yawa, wanda ake iya biya cikin dogon lokaci. Idan Sin tana tabka magudi kan rancen kudi dake baiwa nahiyar, don me ta dauki irin wannan mataki dake iya taimakawa nahiyar wajen raya manyan ababen more rayuwa da kyautata zaman takewar al’umma? Babu wani banki dake son ba da irin wannan rancen kudi saboda babu riba.
Gidan rediyon Deutsche Welle na kasar Jamus ya ba da labari cewa, Sin tana zuba jari ga kasashen Afrika wajen yin kwaskwarima a fannin sadarwar yanar gizo, abin da gwamnatocin wasu kasashen yamma ba su son a gudanar don ba sa son a ingiza bunkasuwar fasahohin nahiyar, amma a shekarun baya-bayan nan, kasashen Afrika da dama suna neman taimakon kasar Sin wajen raya manyan ababen more rayuwa a bangaren yanar gizo. Idan kasar Sin tana son kwace albarkatun nahiyar, to don me take kokarin taimakawa nahiyar wajen bunkasa tattalin arziki da ingzia ci gaban kimiyya da fasaha, abin da zai taimakawakasashen Afrika wajen kara karfin dogaro da kansu wajen samun bunkasuwa? Kowa ya sani, wata kasa maras karfi ta fi saukin fadawa hannun sauran kasashe masu karfi.
Jaridar The Washington Post ta ba da wani bayani cewa, a cikin shekarun da suka gabata, wasu ‘yan siyasar Amurka na kokarin bayyana ra’ayinsu na kin jinin kasar Sin, matakan da suka dauka sun hada da yin bincike kan hadin kan Sin da Afrika, har sun yada jita-jita game da wannan batu duk da cewa ba su da wata shaida. Sun mai da jami’ai ko kamfanoni dake da alaka da Afrika matsayin masu kwace albarkatu, saboda haka ‘yan Afrika na cikin mawuyancin hali. Abin da The Washington Post ya fadi ya sheda cewa, tabka magudi wajen bayar da rancen kudi da kwace albarkatun Afrika hujja ce mara tushe da ‘yan siyasar kasashen yamma suke amfani da ita.
Wasu ‘yan siyasa da kafofin yada labarai nakasashen yamma suna kokarin bata hadin kan Sin da Afrika da nufin hana kasar Sin ta shiga kasuwar Afrika, sabo da kamfanoninsu ba su son su yi takara da kamfanonin Sin, ta yadda za su kiyaye moriyarsu. Ban da wannan kuma, suna son hana neman cin moriyar juna tsakanin kasashe masu tasowa, suna yunkurin bata dangantakar kasashe masu tasowa, don hana bunkasuwarsu.
Ci gaban da aka samu ta fuskar hadin kan Sin da Afrika na a zo a gani ne a nahiyar, abin dake amfanawa zamantakewar al’ummar Afrika a bangarori daban-daban, jama’ar Afrika su kadai suka san nagartattun ci gaban hadin kan bangarorin biyu. Afrika na matukar bukatar hadin kai da sahihan abokai, matakin dake iya taimaka mata wajen samun bunkasuwa mai dorewa. (Amina Xu)