logo

HAUSA

China na ci gaba da ba da tabbaci ga farfado da tattalin arzikin duniya

2021-09-15 21:33:19 cri

China na ci gaba da ba da tabbaci ga farfado da tattalin arzikin duniya_fororder_微信图片_20210915213253

A halin yanzu, sabon nau'in kwayar cuta ta Delta na yaduwa a duniya, wanda ya kawo cikas ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Bisa wannan halin da ake ciki, sabbin alkaluman tattalin arzikin da hukumar kasar Sin ta fitar, sun jawo hankalin kasashen duniya a cikin 'yan kwanakin da suka gabata.

Ga kasar Sin, saurin karuwar wasu manyan alamun tattalin arziki ya ragu a watan Yuli, saboda karuwar rashin tabbas na waje, yanayin ambaliyar ruwa a cikin gida, da yaduwar annobar a wasu wurare. Amma, manyan alamu bisa manyan tsare-tsare na kasar, har yanzu suna kaiwa matsayin da ya dace, kuma tattalin arzikin kasar baki daya na ci gaba da farfadowa.

Kamar yadda manazarta da dama suka nuna, kasar Sin za ta ci gaba da zama mai tabbatar da farfadowar tattalin arzikin duniya.

Wasu manazarta sun ce, bisa ga girman kasuwarta, dorewar tattalin arzikinta, da madaidaicin manufofin jaroranci, kasar Sin ba wai kawai ta jure matsin lamba daga waje a fannin hauhawar farashin kaya ba, har ma tana taimakawa duniya don rage matsin lamba a fannin.

Lallai, ga tattalin arzikin duniya dake cike da rashin tabbaci a halin yanzu, tabbatar da farfadowar tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata na da matukar muhimmanci. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, duk da yake ana fuskantar wasu kalubaloli, ciki har da hana dunkulewar tattalin arzikin duniya da ba da kariyar cinikayya, a ko da yaushe kasar Sin tana bude kofarta ga waje, kuma tana ci gaba da fadada budewa don taimakawa tattalin arzikin duniya wajen samu farfadowa, daga tasirin yaduwar annobar cikin gaggawa. (Mai fassara: Bilkisu)