logo

HAUSA

Kaso 2 na alluran COVID-19 kadai aka yi amfani da su a nahiyar Afrika

2021-09-15 10:28:50 CRI

Kaso 2 na alluran COVID-19 kadai aka yi amfani da su a nahiyar Afrika_fororder_210915F2-allura

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce an bar nahiyar Afrika a baya, bisa la’akari da cewa, kaso 2 cikin dari na allurai sama da biliyan 5.7 na riga kafin COVID-19 da aka yi amfani da su a duniya kadai nahiyar Afrika ta dauka.

WHO da Tarayyar Afrika da shirin COVAX, sun kira ga masu samar da riga kafi da su ba shirin COVAX muhimmanci, tare da bukatar kasashe su cika alkawarin da suka dauka na raba alluran da saukaka musayar fasahar samarwa da hakkin mallakar rigakafin.

A watan Augusta, WHO ta yi kira da a haramta bayar da riga kafin a zagaye na 3 na wucin gadi, domin mayar da hankali kan mutane mafi fuskantar hatsari a fadin duniya, wadanda ba su kai ga samun riga kafin na farko ba. (Fa’iza Mustapha)