logo

HAUSA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ta Moriyar Juna ce Da Samun Nasara Tare

2021-09-15 17:53:12 CRI

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ta Moriyar Juna ce Da Samun Nasara Tare_fororder_A

Yayin da wasu sassa ke yaba hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, a hannu guda kuma wasu kasashen yammacin duniya na yiwa hadin gwiwar wata irin bahaguwar fahimta, ta hanyar yada bayanan boge don ganin sun bata wannan hadin gwiwa, inda suke yada karyar cewa, wai, bangaren Sin ne kadai yake amfana da hadin gwiwar. Dokin mai baki aka ce ya fi gudu

Sanin kowa ne cewa, Turawan yamma sun dade suna mulkin mallaka a galibin kasashen nahiyar Afirka, kuma duk tsawon lokacin da suka kwashe a irin wadannan kasashe, babu abin da suka tabuka, sai kwashe albarkatu da ma muhimman kayayyakin tarihin wadannan kasashe, wadanda a halin yanzu suka baje kolinsu a dakunan suna adana kayan tarihi, ba kunya ba tsoron Allah. Sun kuma bar irin wadannan kasashen nahiyar ba tare da wasu muhimman kayayyakin more rayuwa ko wani tsari na ci gaba ba.

Amma bayan kulla huldar moriyar juna tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, sassan biyu sun amfana matuka daga dukkan fannoni. Misali, a lokacin da kasashen Afirka ke karkashin mulkin mallakar Turawan yamma, iyayen gijin nasu kan ba su bashi ne ta hanyar gindaya musu wasu sharudda, ko dai su rage darajar kudaden kasashen su kowa su ka’idoji da ya shafi muhimman muradun kasashen, amma rancen da kasar Sin take samarwa kasashen Afirka, masu saukin biya ne, ba kuma tare da gindaya wani sharadi ba, a wasu lokutan ma, ta kan yafe musu basussukan kokara musu wa’adin biya, saboda wasu dalilai na musamman har ma ta kan nemi hukumomin kudade na kasa da kasa, kamar babban bankin duniya da asusun bayar da tallafi na duniya IMF, da kodai su yafewa kasashe masu tasowa bashin da ake bin su ko a kara musu wa’adin biya. Haka, yanzu kasar Sin na sayan kayayyaki daga nahiyar da ma tallata su ta kafar intanet da sauran su. Abin tambaya a nan shi ne, Idan har bangaren Sin ne kadai yake amfana da wannan hadin gwiwa, me ya sa zai nemi a yafewa kasashen Afirka bashin da ake binsu?. Sin da Afirka suna hadin gwiwa ne, don su gudu tare su tsira tare.

Bisa tsare-tsaren dake kunshe cikin hadin gwiwar sassan biyu, kasar Sin da Afrika, sun hada karfi da karfe, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, da nufin samar da dangantaka mai karfi da ba a taba ganin irinta ba, tsakanin kasar dake nahiyar Asiya da kuma nahiyar Afrika, wadanda yawan al'ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al'ummar duniya baki daya. Bayan tsawon shekaru na kyakkyawar alakar dake tsakanin bangarorin biyu, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da nahiyarAfrika a fannoni da suka hada da tattalin arziki, Ilimi, cinikayya, kayayyakin more rayuwa, al'adu, noma, raya masana'antu da ma kaiwa juna ziyara a bangaren manyan jami'ai da ma shugabanni. Sai uwa uba rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen juna da marbata muhimman muradunsu

Tarukan dandalin hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afrika FOCAC, da suka gudana a biranen Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Beijing na kasar Sin gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Wadanda ke aikewa da muhimmin sako ga al'ummomin duniya cewa, Sin da Afrika sun hada hannu don samun nasara tare.

Ana sa ran, kasashen Afrika da Sin za su hade manufofin da dabarunsu na samun ci gaba karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da muradun ci gaba masu dorewa na MDD da kuma ajandar raya nahiyar ta kungiyar Tarayyar Afrika nan da shekarar 2063. Alakar sassan biyu, tana kara taka muhimmiyar rawa a fannonin rayuwar bil-Adam, matakin da masana suka yaba matuka. Masu iya magana na cewa fahimta fuska, kowa da yadda zai fahimci wannan hadin gwiwa. Amma dai dukkan sassan biyu, wato Sin da Afirka, sun fi kowa sanin irin fa’idar da suke girba daga wannan hadin gwiwa mai tarin muhimmanci. Wai mai Daki shi ya san inda yake masa Yoyo. (Ibrahim Yaya)