logo

HAUSA

Duk mai neman bata alakar Sin da Afirka ba zai yi nasara ba

2021-09-15 09:14:39 CRI

Yadda Sin da Afirka ke amfana daga hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta sa wasu kasashen yamma na yada labaran karya tare da yiwa hadin gwiwar bahaguwar fahimta. Sanin kowa ne cewa, Sin da Afirka sun dade suna hadin gwiwa a fannoni daban-daban, kuma yanzu haka sassan biyu sun kasance aminan juna na kwarai.

Duk mai neman bata alakar Sin da Afirka ba zai yi nasara ba_fororder_210915世界21034-hoto2

A duk tsawon hadin gwiwarsu, Sin da Afirka suna martaba muhimman muradun juna, kamar rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen juna, da goyon bayan juna duk wahala duk dadi da sauransu.

Duk mai neman bata alakar Sin da Afirka ba zai yi nasara ba_fororder_210915世界21034-hoto3

Hadin gwiwar sassan biyu ta baya-bayan nan ita ce, alluran riga kafin COVID-19, baya da samar da kayayyakin more rayuwa, kamar samar da hanyoyin mota da layin dogo, da tashoshin jiragen sama da na ruwa da rukunonin masana’antu da sauransu.

Duk mai neman bata alakar Sin da Afirka ba zai yi nasara ba_fororder_210915世界21034-hoto4

A dalilin wanan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kasashen nahiyar sun amfana da abubuwan da dama, kamar horas da ma’aikata da jami’an lafiya da yadda kasar Sin take tura rukunonin jami’an lafiya zuwa kasashen Afirka a lokuta daban-daban da samar da guraben karo ilimi. Tarukan dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da suka gudana a biranen Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, da Beijing na kasar Sin, gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin bangaorin biyu. Wadanda ke aikewa da muhimmin sako ga al’ummomin duniya cewa, Sin da Afirka, sun hada hannu don samun nasara tare. Don haka, duk mai neman bata wannan alaka, tabbas, ba zai yi nasara ba. (Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)