logo

HAUSA

Kotun Musamman Ta Uyghur Shirme Ce Dake Take Nasarorin Da Aka Samu A Fannin Yaki Da Ta'addanci A Duniya

2021-09-14 21:43:32 cri

Kotun Musamman Ta Uyghur Shirme Ce Dake Take Nasarorin Da Aka Samu A Fannin Yaki Da Ta'addanci A Duniya_fororder_微信图片_20210914213827

Ranar 13 ga wata bisa agogon wurin, aka kammala zaman sauraron ra’ayi na biyu na abin da ake kira wai “Kotun Musamman ta Uyghur” a kasar Burtaniya. Wadanda ba su sani ba suna iya tsammanin cewa wannan kotu ce, amma a hakika dai, ba ta da tushe bisa dokokin kasa da kasa, da kuma tasiri ko kadan. Kotu ce ta bogi. Abin da ake kira “zaman sauraron ra’ayi” ma a hakika ba a gudanar da shi bisa tsarin shari'a ba, illa dai wani shirme ne da kasar ta tsara don nuna adawa da kasar Sin.

A cewar rahotannin, wata kungiya ce mai zaman kanta da aka kafa a Burtaniya a matsayin kamfani mai zaman kansa, wanda aka iyakance ayyukan sa bisa tabbaci da yake da shi, kuma yawancin tallafin kudi da ya samu sun fito ne daga majalisar World Uyghur Congress wato WUC a takaice, wadda ke adawa da kasar Sin, da bin ra’ayin janyo baraka ga kasa. Tun lokacin da aka samar da ita, majalisar WUC tana da alaka da kungiyar ta'addanci ta ETIM, kuma ta tsara ayyukan ta'addanci na balle jihar Xinjiang daga kasar Sin. Idan an kara duba asalinta, za a gano cewa, majalisar na samun goyon baya ne daga asusun NED na kasar Amurka.

A bayyane take, abin da ake kira “Kotun Musamman ta Uyghur” kayan aiki ne na adawa da kasar Sin, kuma “Zaman sauraron ra’ayi” har yanzu yana wasa ne bisa tsohuwar hanyar “haifar da karairayi game da Xinjiang”.

Abun lura a nan shi ne, wannan “Kotun Musamman ta Uyghur” ta gudanar da “zaman sauraron ra’ayi” na biyu ne a daidai lokacin da kusan bikin cika shekaru 20 da kai harin ta'addanci na “9.11”. Masu adawa da kasar Sin suna kaddamar da jita-jita da batanci kan jihar Xinjiang, a wannan lokaci ba wai kawai sun tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasar Sin ba ne, har ma a bayyane take suna take nasarorin da aka samu ne a yaki da ta'addanci a duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)