logo

HAUSA

Tian Guiying: Mace ta farko da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin

2021-09-14 09:39:44 CRI

Tian Guiying: Mace ta farko da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin_fororder_Tian Guiying1

Tian Guiying, ita mace ta farko ce da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin a 1949. Ta samu lambar karramawa a matsayin nagartacciyar ma’aikaciya ta kasa, wadda ta karba daga shugaba Mao Zedong a 1950. Tian ta fuskanci wahalhalu da dama, a kokarin cimma burinta, haka kuma ta zama abun koyi ga dubban mata matasa. Ana rubuta labarin rayuwar Tian Guiying da nasarorin da ta cimma cikin littattafai a wancan lokaci, wadanda daga baya, suka zama tubalin fim na kasar Sin na farko game da masana’antar sufurin jiragen kasa, mai suna Mace Direba.

Tian Guiying: Mace ta farko da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin_fororder_Tian Guiying2

Tian Guiying na son kallon tsoffin hotunanta a duk lokacin da take hutawa. Ta kafa hotunan da ta fi so a muhimman wurare a gidanta. Wani hotonta ne a lokacin da ta hadu da shugaba Mao Zedong, yayin da wani ke nuna ta zaune a taragon jirgi, tana kallon waje ta taga, kuma tana sanye da farin kyalle a wuyanta.

A duk lokacin da take ba da labarai, Tian Guiying mai shekaru 90 da haihuwa na iya tunawa sosai da lokacin da take matashiya cike da kuzari.

An haifi Tian ne a 1930, mahaifinta masunci ne mai karancin kudin shiga, kuma sun yi rayuwa a yankin Lvda da yanzu ake kira Dalian, wani birni dake lardin Liaoning na arewa maso gabashin kasar Sin. Tian na da yayye mata 5. Dukkan iyalin sun dogara ne kan sana’ar mahaifin na kamun kifi.

A lokacin da ta kai shekaru 12, Tian ta samu damar shiga makaranta, amma kuma sai ta daina zuwa bayan shekaru 2 saboda matsalolin kudi da iyayenta ke fuskanta. Daga nan sai ta fara aiki a wata masana’antar buga takardu, a matsayin mai koyon aiki, a lokacin da ta kai shekaru 15 kuwa, sai aka dauke ta aikin sayar da tikiti a wani dakin cin abinci na tashar jiragen kasa dake Dalian.

A lokacin da ba ta da aiki, Tian Guiying ta kan je makarantar dare da tashar jiragen ta kafa. Tana matukar son koyo daga littattafai, lamarin da ya taimaka wajen fadada tunaninta. Da tafiya ta yi tafiya, sai ta kara zage damtse domin hidimtawa kasarta, kuma wannan jajircewa ta kara karfi bayan ta ga irin nasarorin da Sin ke samu.

“Muddin zan koyi fasahohi, zan iya yin komai”, cewar Tian. Bayan ganin jajircewa da burin Tian, sai shugaban tashar ya tura ta koyon tukin karamin jirgin kasa.

Tian Guiying: Mace ta farko da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin_fororder_Tian Guiying3

Tian ta taba ganin hoton wata mace ‘yar Tarayyar Soviet dake tuka jirgin kasa a ofishin ma’aikatan tashar. Matar ta ba ta sha’awa, inda ta yi burin koyi da ita wata rana.

A 1949, Tian ta samu wani labari mai dadi, wato kasar Sin ta shirya horar da rukuni na farko na direbobi mata na jirgin kasa a tashar jiragen kasa ta Dalian, kuma tana daukar wadanda suke da sha’awa.

A lokacin, mata kalilan ne ke aiki a wurin. Tian na son zama daya daga cikin wadanda za su yi rajista. Amma da ta tattuna batun da iyayenta, gwiwarta ta yi sanyi. “Aikin tukin jirgin kasa na da wahala sosai. Bai dace da ‘ya mace ba”, cewar iyayenta.

Sa’ar Tian Guiying ita ce, yayunta sun goya mata baya. Bayan tunani mai zurfi, Tian mai shekaru 19 ta yi watsi da adawar da iyayenta suka nuna, ta cike form na neman shiga shirin karbar horon.

Bayan zaben da aka yi bisa matakai masu tsanani, sai aka zabi Tian Guiying da sauran wasu ‘yan mata 8. A lokacin, jirage na amfani ne da kwal. Don haka, mataki na farko na zama direban jirgin kasa shi ne, yadda za a kunna wuta, da tabbatar da ta ci gaba da ci ta hanyar zuba mata kwal.

An horar da matan ne ta hanyar amfani da wani jirgin bogi, inda aka ba su aikin zuba kwal domin wutar ta ci gaba da ci. Aikin na da wahala sosai, kuma a ko da yaushe matan na jike da gumi da kuma gajiya. Tian kan ba sauran kwarin gwiwa, ta ce, “komai na da wahala da farko. Idan muka tsallake wannan mataki, za mu samu nasara.”

Don haka, ‘yan matan suka rika karfafawa juna gwiwa, kuma suka zage damtse. Nan da nan, hannayensu suka yi kanta.

Tian Guiying: Mace ta farko da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin_fororder_Tian Guiying4

Duk da cewa yanzu shekaru 72 ke nan, Tian na tunawa da duk abun da ya faru a lokacin horon, da sauran darrusan da aka koyar da suka fi ba Tian wahala.

A ko wanne dare, bayan sun koma daki, su kan tattauna darussan, ba kwanciya barci har sai sun fahimci dukkan abun da aka koya musu a ranar, ko da kuwa lokacin kashe wuta ya yi, Tian kan yi karatu ta hanyar amfani da tocilan.

Daga bisani, kwalliya ta biya kudin sabulu. Watanni biyu daga nan, ta cinye jarrabawa tare da sauran matan. An dauke ta aiki, a wani wa’adi na wucin gadi a matsayin direbar jirgin kasa.

Bisa horon wani babban direba, Tian ta yi saurin lakantar dabarun tuki, ta zama cikakkiyar direba.

Tian Guiying: Mace ta farko da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin_fororder_Tian Guiying5

An gudanar da bikin gabatar da direbobi mata na jirgin kasa na “March 8th Women Train Crew,” da ya kunshi mata 9, a dandalin dake gaban tashar jirgin kasa ta Dalian. An yi bikin ne a ranar 8 ga watan Maris na 1950. An yi wa jirgin da suka yi aiki da shi lakabi da “March 8th”. Tutar da aka ba su na dauke da kalmomin “jirgin mata”. A cewar Tian, “ba zan manta da wannan rana ba, ina tunawa da ita tsawon rayuwata.”

A wannan rana, Tian mai shekaru 20, ta yi tafiya ta farko a matsayin direbar jirgin kasa. Ta tuka jirgin daga Dalian zuwa Lvshun, wata gunduma dake Dalian. Bayan ta shiga mazaunin direba, Tian ta sanya kayan direba a karon farko, ta nuna kwarewa tare da mayar da hankali. Bayan buga ham, mace direban jirgi na farko a kasar Sin ta fitar da jirgin daga tasha, da wannan, Tian ta bude wani sabon babi a tarihin sufurin jiragen kasa na kasar Sin.

A washegari, jaridar People’s Daily ta wallafa wani sharhi mai taken “karon farko a bangaren sufurin jiragen kasa na al’umma, mace ‘yar Dalian Tian Guiying ta tuka jirgin kasa”. Labarin da ya ja hankalin mutane da dama a fadin kasar.

A wannan lokaci, galibin mutane sun dauka maza ne kadai za su iya tuka jirgin kasa. Amma saboda jajircewa da kwazo, Tian Guiying tare da sauran mata 8 ba kawar da wannan tunani tare da tabbatar da “mata za su iya tuka jirgin kasa” kadai suka yi ba, har ma da karfafawa mata daga dukkan bangarori gwiwar jajircewa da ba da tasu gudunmuwa ga al’umma.

“Muddin za mu iya jure wahalhalu da yin aiki tukuru, mata za su iya yin komai,” cewar Tian Guiying. Yayin da ta kusa cika shekaru 3 a matsayin direba, jirgin mai lakabi “March 8th” ya yi tafiyar sama da kilomita 200,000 ba tare da hatsari ko sau daya ba.

Tian Guiying: Mace ta farko da ta kasance direbar jirgin kasa a kasar Sin_fororder_Tian Guiying6

An fitar da shirin fim mai suna Direba Mata ne a fadin kasar Sin a 1951, wanda ya mayar da hankali kan labarin Tian Guiying, kuma ya karfafawa mata matasa gwiwar hidimtawa kasa. Bayan bayyanar fim din, sunan Tian ya karade kasar Sin, inda ta zama abar koyi ga mata masu tarin yawa.

A yanzu, za a iya ganin mata Sinawa suna aiki a bangarorin daban-daban, wanda ke nuna cewa, ba abun da matan kasar Sin ba za su iya ba. 

Kande